@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA 'YAN KADAN ALLAH KE YIN ALFAHARI
Duk wani yabo cikin Alqur'ani da za ka ji , to, da 'yan kadan ake yi, yafiya yawa kuma zargirsu ake yi.
Wannan kuwa na da alaqa ne da cewa su 'yan kadan din ne suke ganin gaskiya su bita komai wuyarta, kuma komai zargin da za ayi musu, domin su ba sa tsoron zargin masu zargi.
Su kuma mafiya yawa sun fi bin son zuciyarsu da kuma fifita duniyarsu kan lahirarsu. Dalilaina na fadin wannan magana shine, Allah (T)na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇?
?👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ KUMA (lalle)IDAN KABI MAFI YAWAN(mutane)DA KE DORON QASA ZA SU BATAR DA KAI DAGA HANYAR ALLAH .‘’
‘’ SAI DAI MAFI YAWAN MUTANE BA SA YIN IMANI (dagaskiya).‘’
‘’ SAI DAI MAFI YAWAN MUTANE BA SU DA HANKALI (wajen gane gaskiya).‘’
Shi yasa idan ka kalli dukkan gurin da jama'ah suka fi rinjaye sai ka tarar bata ce da biyewa son zuciya.
LATSA NAN👇
☞ ͡Saɓanin Ganin Watan Ramadhan ko Shawwal
☞ ͡Hukuncin wanda yaƙi ɗaukar Azumi, Alhali yana da labarin ganin Wata
☞ ͡Gaskiya da Gaskiya Mun raba kayan abinci Tiraila 276, a jahohi Uku – Minista Sadiya
Su 'yan kadan kuwa da mafi yawan mutane ke yi musu muguwar fassara Allah ya fassara su ne da cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ SAU DA YAWA DAGA CIKIN RUNDUNA (ta jama'a)KADAN NE MASU YIN RINJAYE AKAN RUNDUNAR (jama'a)MASU YAWA DA IZNIN ALLAH, KUMA ALLAH NA TARE DA MASU HAQURI .‘’
‘’ 'YAN KADAN NE KE YIN IMANI (da gaskiya).‘’
‘’ 'YAN KADAN NE MASU HANKALI (wajen fahintar gaskiya).‘’
‘’ 'YAN KADAN NE KE WA'AZANTUWA (daga dukkan wasu misalan da Allah ke bayyanar da su cikinsu don ya zama darasi).‘’
Dan Allah yi nazari cikin wannan rudu da ake ciki, kai cikin wanne aji ka fada, masu yawan da Allah ke zarga ko kuma 'yan kadan din da yake yin alfahari da su?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~24th April, 2020.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi