Yaa Ubangiji ! Kurkuku Ne Mafi Soyuwa Gareni, Daga Abinda Suke Kira Na Zuwa Gare Shi !!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SAYYID ZAKZAKY (H)YAYI KOYI DA ANNABI YUSUF (A.S)

Babu wani Manzo da Allah ya aiko shi ba tare da ya jarraba shi kan wannan aikin da ya aiko shi a kansa ba, sai dai jarrabawar takan zo ne ta hanyoyi daban-dabam.

Wasu akan cutar dasu ne ta hanyar gaba dasu da kuma bin dukkan wasu matakai na ganin an hana su cimma wannan abinda suke kira a kansa. Wasu kuma akan daddake su tare da barazanar kisa.

Sannan wasu akan tattara musu dukkan nau'o'in jarrabawa da ta shafi duka, kisan jama'arsu, lalata musu dukiyoyinsu, sanya su cikin gidan yari (prison)da dai sauransu. Gwargwadon matsayinsu gwargwadon jarrabawarsu.

Sayyid Zakzaky (H)ya kasance cikin wadanda Allah ya tattara musu dukkan wasu nau'o'i na jarrabawar da manya daga cikin Manzanni (A.S)suka samu.

Kafiran Makkah sun so Annabi (S.A.W.W)ya sassauto daga kan matsayin da ya dauka na da'awarsa don suma kafiran su sassauta masa, amma dai bai yi musu biyayya kanwhakan ba.

A yayin da Annabi Yusuf (A.S)yaga ana son karkatar da shi zuwa aikata sabon Allah (T)sai yace,

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ YAA UBANGIJI ! KURKUKU NE MAFI SOYUWA A GARE NI DAGA ABINDA SUKE KIRANA ZUWA GARE SHI .‘’

(Suratul Yusuf, aya 33)

To, irin wannan kira Sayyid Zakzaky (H)ya yiwa Allah yayin da yaga azzalumai na qoqarin tilasta shi kan dole sai ya yiwa tsarin kafirci biyayya.

Cikin tattaunawar da yayi da jami'an tsaro kafin su dawo da shi Kaduna daga Abuja, sun buqaci yayi musu alqawarin barin abinda yake yi na da'awarsa, har suke ce masa da ace za su sake shi, me yake gani zai yi?

Sai yace musu abinda dai suka sanshi a kansa kafin su kama shi. Wannan dalili yasa suka cigaba da tsare shi.

Da ace ya nuna zai yi musu biyayya, to, da basu cigaba da tsare shi ba.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~26th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post