WHO; Ana Kan Gwajin Alluran Magungunan Cutar Corona Fiye Da 50



Hukumar Lafiya ta kasa da kasa ce wacce ta bayyana hakan ta bakin mai Magana da yawunta a Najeritya Fiona Braka

(ROHOTON ABNA24.com) Fiona Braka ta kara da cewa; baya ga allurar rigakfin da ake gwaji, da akwai wasu kasashe da dama wadanda suke kan gwada magungunan warkewa daga cutar.

Ya zuwa yanzu dai mutanen da su ka kamu da cutar ta Covid-19 sun kai 874,615 a cikin watanni uku daga bullar cutar zuwa yanzu. Wadanda cutar ta kuma kashe a wannan tsakanin sun kai 43,430, wadanda kuma su ka warke sun kai 184,952.

Mafi yawancin wadanda su ka warke din dai wadanda su ke da karfin gwarkuwar jini ne da kuma rashin wasu cutuka masu hatsari.

Kasar Amurka ce akan gaba wajen yawan wadanda su ka kamu da cutar ta “Corona” sai kuma kasar Italia da take bin ta a baya.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post