Cuta Da Magani
Yanda zaku Bambance Tsakanin Cutar corrona virus dasauran Rashin Lafiya.
Gabatarwa :
-Kasantuwar akwai kamanceceniya tsakanin alamomin cutar koronabairos da sauran rashin lafiya, hakan yasa mu ka fitar da wannan rubutu domin samun natsuwa da kuma iya bambance me ke damunmu a lokacin da mu ka ji wadannan alamomi.
-Ga jerin nau`o`in rashin lafiyar da suke da alamomi masu kama da alamomin cutar koronabairos:
1. Air Pollution.
2. Flu.
3. Common Cold.
4. Corona Virus (Covid-19).
Ga bayanansu a takaice kamar haka:
1. Air Pollution: Gurɓacewar iska kan haifar da wasu alamomi masu kama da na Covid-19 ga alamomin kamar haka:
* Dry Cough: Wato tari mai sarke mutum.
* Sneezing: Wato Atishawa ko Hantsirwa.
-Flu: Ciwon sanyi shi ma yana da alamomi har guda shida masu kama da na COVID-19.
KARANTA WANNAN: Tambaya: Shin jami'an tsaro na tsare kamuwa da cutar Coronavirus ne?
ga dai alamomin kamar haka:
* Cough with Mucus: Tari da Majina.
* Sneezing: Atishawa ko Hantsirwa.
* Runny Nose: Tsiyayar majina ta hanci.
* Body ache: Ciwon jiki.
* Weakness of the body: Rashin karfin jiki.
* Light fever: Matsakaicin zazzabi.
3. Common Cold: Shi ma wannan yana da alamomi guda uku, ga su kamar haka:
* Cough with Mucus: Tari da Majina.
* Sneezing: Atishawa ko Hantsirwa.
* Runny Nose: Tsiyayar majina ta hanci.
4. Corona Virus (Covid-19): Koronabairos na da dukan alamomin cutukan da mu ka ambata a sama har guda shida; ga su dai kamar haka:
* Dry Cough: Busasshen tari.
* Sneezing: Atishawa ko Hantsirwa.
* Weakness of the body: Rashin karfin jiki.
* High fever: Zazzabi mai tsanani.
* Difficulty in Breathing: Wahalar shakar numfashi.
-Duk wanda ake zargin ya kamu da Koronabairos a tuntubi wannan lambar kamar haka:
-080097000010 NCDC Nigeria.
Manazarta
Pathology Department AIIMS, Delhi India.
Fassarar
-Dent Faisal sani Modibbo Gozaki.
-modibbogozaky@gmail.com
-08063607225
Tags:
Cuta da Magani