@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SUN JAHILCI AL'AMARIN MAHDI (A.F)
Shi ilimi ana tsammanin samunsa ne wajen me nemansa, haquri kuma a same shi tare da me yinsa.
Sai dai wani abin al'ajabi shine, mafi yawan masu karatu sun jahilci wanene Imam Mahdi (A.F), ta fuskacin nasabarsa, matsayinsa da kuma haqqinsa a kansu.
Wannan jaliltar al'amari nasa yasa su yin baganniya cikin duhu da sunan wai suna bayani a kansa, domin sun tabbatar akwai bayaninsa, sai dai sun kasa sanin haqiqanin shi wanene.
KARANTA WANNAN👇
➝Imam Mahadi (Ajtfs) Fita Na Biyar (5)
➝Non Communicable Diseases Part (1)
➝Covid-19 da Gwamnatin Nijeriya – Nazari
To, gaskiyar lamari dai shine, asalin su masu karatu wadanda ake yin karatu a wajensu suna gaba ne da gidan Annabi (S.A.W.W)ta hanyar shan ruwan qiyayya daga magabatansu, wannan dalili yasa ba sa bayyanar da haqiqanin gaskiya ga masu nemanta. Su kuma masu neman gaskiyar sun saki hanyar gaskiya, domin ba sa nemanta wajen masu ita.
Wannan dalili yasa za kaga mutum na tunqaho da tarin littattafan karatu da sunan wai ya karanta, amma kuma bai gano shiriya a cikinsu ba.
Saboda haka ne yasa da zarar sun bude baki da sunan yin magana ta addini sai su ba ka dariya, domin za ka ji babu hikima ko fasaha cikin zantukansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~10th April, 2020. KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi