Wannan harka tana koyar da mu riƙon amana ne!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MATA SUN FI RIQE AMANA FIYE DA MAZA

Kafin ka sami mata uku da suka juyawa maza baya sai ka sami 10 da suka juyawa mata baya. Wannan kuwa na da alaqa ne da qarancin rashin riqon amana daga maza, domin za su iya son mace yanzu, amma qanqanin abu yasa su juya musu baya.

Sayyid Zakzaky (H)na qarfafarmu da riqon amanar junanmu da taimakon junanmu, shi yasa ma ya gargade mu kan auri ka gyara ta hanyar barin sistocin da muke tare da su.

Sanin kowa ne ita wannan harka akwai manya-yanyan jarrabawowi cikinta wadanda za su iya mayar da mai kudi talaka, lafiyayye ya zama naqasasshe, mai ilimi ne kawai bai zai iya dawowa ya zama jahili don wata waqi'ar da ta same shi ba.

Yana da sauqi namiji yayi haqurin zama da matarsa idan ta hadu da wata lalurar jinya ta hanyar waqi'a, amma shi yafi sauqi ya juya mata baya in dai ta sami lalura kafin ta zama matarsa, (wato lokacin tana matsayin budurwa)gare shi.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Tunaninsa shine akwai 1000 kyawawa masu lafiyar jiki ko cikar halitta, saboda haka sai su basu haquri su koma kan wasu mata na dabam.

Wannan abu yana da wuya ka same shi cikin mata, domin su suna da haquri da riqon amana da cigaban soyayya da zama tare da mazaje ko samarinsu da suka hadu da wata lalura.

Saboda haka mu canza tunani 'yan'uwa, idan aka ce za mu gujewa sisters don sun hadu da wata lalura, to, a tunaninmu kuma su waye za su aure su tunda mu mun qi su?

Babu abinda waqi'a ba za ta iya haifarwa ba, domin da dama sun rasa rasa wasu bangarorin jikinsu sanadin waqi'o'i.

Ba wai cewa nake ka je ka nemi wacce ke da lalura ba, amma dai kada kace za ka qauracewa sister don ta hadu da wata lalura.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~21st April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post