jiya Inna sauraron rediyo, sai naji ance, kisan da hukuma taiwa ƴan ƙasar ta, adadin yafi wanda Wanda Corona virus tayi!!!
In banda gwamnatin Nijeriya wacce gwamnatin ce zatai haka?
Sannan naga wani video a WhatsApp shikuma na yarda ake rabon abinci, idan kaga video ɗin sai kasha mamaki yanda ake turereni ya wajan ƙarɓar buhu ɗaya na abinci!!!
Wanda nasan silar wanan Turai rai niyar wani yana iya rasa rayin sa!!! To inde silar rabon buhu ɗaya na shinkafa za'a rasa rai, wanda ance Allah yace da akashe rai ɗaya ganda a rusa ɗakin Ka'aba.
Banyi mamaki ba, tunda bawai namanta irin yadda sojojin kasar Nijeriya sukayi akan ƴan uwa ba, a shekararun baya, domin su a kwana uku saida suka zubar da jini sama da jinin mutum 1000.
Gashi basu saka tausayi ba' domin naji ance akwai wata mata, da aka harbe ta' atake ta haihu a gurin, Amman baka aka ƙara Harbin jaririn.
Hakanan wani yaro ƙarami shima an harbi baban sa, sai ya taso yataho gurin sojan yana kiran sa da baban sa, sai kawai ya saka bindiga ya harbe shi.
Arhali ko ayaƙi ba'a kashe yara da mata.
Sannan haka suka kunna wuta, suna ƙone mutane, da ran su batare da tausayi ba.
Ni abinda yafi bani haushi shine yadda wasu hausawa ƴan Nigeria,sukai murna bisa irin wannan baƙin zaluncin da akai.
Duk wanda ya iya murna da kisan da akai tabbas idan yasamu bindiga da cikakkiyar dama kila shima yana iya harbin.
Nasan koda zakzaki ba musulmi bane, to tabbas Allah zai saka masa, tunda shi Allah baison zalinci,Kuma ko kafiri aka zalunta Allah zai saka masa.
Tags:
Muhimman zantuka