@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH BA YA JIN KUNYA GAME DA GASKIYA
Fadin gaskiya haqqi ne da ya hau kan dukkan musulmi ko kuma nace dukkan mai imani musulmi yake ko kirista, domin Allah (T)ne ya umarce mu kan haka.
Fadin gaskiya kan abu shine adalci, da za a sami wani mutum yayi ba daidai ba, sannan kai ka fito kana nuna cewa abinda yayi daidai ne, to, wallahi kai ba ka zama cikakken mutum mai adalci. Ajiye komai yadda yake shine adalci.
Tabbas, duk wani rubutu nawa da nayi kan wani mutum, to, matuqar za kayi min adalci ba za kace nayi masa sharri ko na zage shi ba. Na kanyi iya qoqarina wajen kiyaye abinda zan fada ko na rubutu game da wanni don neman kubutar da kaina qajen Allah.
Kuma ina tsoron tuhuma daga mutane don kada na kasa kare abinda na rubuta, domin hakan shi zai kare min mutuncina.
KARANTA NAN👇👇
◉Ka dakatar da karbar kudin wuta da ruwa na tsawon wata biyu–Cewar wani Dan Majilisa
◉Mai nisan kwana zaiga ƙàrshen wannan zaluncin da idon sa
◉Tsoro bala'i ne, Jama'a banda tsoro!!
Fadin magana ba tare da iya kare ta ba in an tuhumi mutum kan zama abin zargi ko tozarta a idon duniya.
Saboda haka, idan nayi wani rubutu(post)yakan farantawa wasu rai, wasu kuma yakan baqanta musu rai don bai yi musu dadi ba, alhali kuwa gaskiya ce wacce mutum bai isa qaryatawa ba. Su irin wadannan mutane masu cewa ina ba su mamaki, ba akan komai bane sai dai don fadin gaskiya wacce su a fahintarsu bai kamata na fade ba, amma ba wai don qarya bane.
Allah (T)ne ya umarce mu da fadinta komai dacinta, kuma ko wacce irin fassara za ayi mana, domin Allah na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ KUMA ALLAH BA YA JIN KUNYA GAME DA (fadin)GASKIYA .‘’
Saboda haka ina ba ku haquri bisa kawo muku abinda ba kwa so na gaskiya, domin yin hakan shine sauke haqqin da ya hau kanmu.
F
R
E
E
S
A
YYID ZAKZAKY (H)!
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~2nd April, 2020.
Tags:
Muhimman zantuka