Ummah Zeenat Mai Halin Annabawa






Abbagano✍

Bani da ɗa (yaro) balle nasan irin soyaiyar da uwa takewa ɗan ta, sede kuma nasan yadda mahaifiya ta take mutukar sona.

Nasan Mahaifiya ta,tana mutuƙar sona, hakanan bata son ko ɓacin raina' balle ace ga wani abu yasame ni.

Sai na auna na hango ummah zeenah itama tana da ƴaƴa, amman yanzu babu su.

Ni bawani karatu nayi ba' sannan bawani ƙoƙari ne dani ba, haka babu wani mataki dana taka, amman a hakan mamana ke mutukar sona.

Sai na auna ƴaƴan Malama zeenah gaba ɗayan su babu irina, dukkan su wandan da duniya zatai alfahari dasu ne, saboda ilimin da suke dasu.

a hakan a shekarun baya aka zo a rana ɗaya aka kashe mata ƴaƴa har guda uku!!! Kisan ma na wulaƙanci!!!

Don ance Sayyid hameed wuƙa akasa aka dinga Chaka masa a goshin sa har Allah yakarɓi abinsa.

Bayan shekara 1 da kashe mata ƴaƴa uku ne, aka sake taho wa har gida, a gaban ta aka harbe mata ƴaƴan ta Uku.

Suma anyi musu kisa na muni, domin Sayyid humaid a gaban ta aka harbo bullet ya Yanka wuyan sa,nan yafaɗi a gaban ta.

ƴaƴa shida, tarasa, kuma duk an kashe su kisan gilla' batare da sunyi laifin komi ba'.

Duk da haka an harbi mujinta, wanda tace ita batana ɗaukar sa miji bane, tana ɗaukar sa jagora, to yaya zakaji idan aka harbi jagoran ka a gaban ka!!!

Ita kanta anmata harbi a jikin ta akalla sama da gu 3' wanda zancen da ake yanzu bata iya tafiya da kafar ta saidai a tukata a keke.

Sannan anzo an katange geta a guri ɗaya tsawon shekara 4 babu zuwa ko'ina.

Shin yaya kake jin idan aka kulleka guri ɗaya babu zuwa ko'ina tsawon kwana 4 kawai?

Shin yaya kake ji idan wani naka yarasu' koda mutuwar rashi. Lafiya ce bawai kisan gilla ba?

Shin ya kake ji idan da ciwo jikin ka' wanda yake hanaka tafiya ?

Shin yakike ji idan akace ga mijin ki kwance gaban ki babu lafiya?

Allah ka karawa Malama zeenah hakuri da juriya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post