Tunisia: An Bankado Wani Shirin Kai Hare-Haren Ta’addanci

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a kasar Tunisia sun bankado wani shirin kungiyar Daesh na kai wasu munanan hare-hare a kasar.

(ROHOTON ABNA24.com) Ma’akatar harkokin cikin gidan kasar Tunisia ta sanar a jiya cewa, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a kasar, sun samu nasarar bankado wani shirin kai harin ta’addanci da kungiyar ‘yan ta’addan daesh ta shirya a cikin kasar.

Bayanin ya ce an samu nasarar cafke mutumin da shi ne zai aiwatar da harin, inda a halin yanzu yake harhada kayayyaki da kuma sanadaran za a yi amfani da su wajen kaddamar da harin.

Bisa ga bayanin da hukumar ta samu daga mutumin da aka kame, wanda mamba ne na kungiyar daesh, ya tabbatar da cewa suna da shirin kai harin ne a cikin watan Ramadan, kuma sun yi amfani da wannan damar ne a halin yanzu, lokacin da gwamnati da jami’an tsaro suka shagaltu da batun corona, domin yin cikakken na kaddamar hari mafi muni.

Jami’an tsaron dai su ne suna ci gaba da bin kadun lamarin, domin tabbatar da cewa an samu nasarar damke dukkanin wadanda suke da hannu a cikin shirin.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post