Matar mai suna Hassanzadeh daga yankin mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, ta warke daga cutar bayan jiyyar kwanaki 27
(ROHOTON ABNA24.com) manajan asibitin da aka kwantar da matar, Sahpur Badiee ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; An kwantar da matar ne a asibiti a ranar 5 ga watan Maris, da aka gwada ta aka same ta tana dauke da cutar ta Corona.
Diyar matar, mai suna Sadeedah, ta ce duk da cewa mahaifiyar tata tana fama da cutar koda a lokaci da corona ta kama ta, amma kuma ta warke garas ba tare da cutar ta karawa kodar tata illa ba.
Tuni dai aka sallami malama Hassanzadeh daga asibitin Imam Riza (a.s) da ke birnin Mashhad inda ta koma gida.
Tags:
Labaran Duniya