Kowa dai ya san cewa kasar da tafi ko ina shiga tashin hankali sanadiyyar annobar Coronavirus a duniya, ita ce Amurka. Yanzu haka akwai kimanin mutane 500,000 da suka kamu da cutar a kasar, inda kuma kimanin mutane 15,000 suka mutu a kasar.
Sama da mutane miliyan daya da rabi sun kamu da cutar, sannan kuma kimanin mutum 90,000 sun mutu sanadiyyar cutar.
A wata hira da yayi da Fox News akan barkewar annobar a kasar ta Amurka, shugaba Donald Trump ya bayar da wata shawara ga al’ummar kasar ta Amurka, inda ya ce: “Kowannen mu yana da gyale saboda haka ina ganin cewa ita ce hanya mafi sauki, idan mutane suna so suyi amfani da shi bani da ikon cewa kada su saka.”
Masu hasashe sun bayyana cewa Trump yana nufin Hijab da Niqab ne amma kuma baya so ya fito ya bayyana ainahin abinda yake nufi shine yasa yace gyale.


Haka kuma a cikin hirar Trump ya kara da cewa “Za ku iya amfani da gyale ko kuma duk wani abu da kuke ganin zaku iya rufe fuskarku da shi, ba wai dole sai takunkumin fuska ba.”

Kasar Amurka ce kasa ta uku a nahiyar Turai da suka hana sanya gyale ko hijabi kafin zuwan annobar Coronavirus, inda kuma yanzu ta zama kasar da take nuni ga al’ummarta su sanya su domin kare kansu saboda karancin takunkumin fuska da ake samu a kasashen duniya.
A yanzu haka dai a kasar ta Amurka kusan ya zama doka mutum ya rufe fuskar shi, inda idan aka kama mutum ba tare da abin rufe fuska ba za a iya cinshi tarar kimanin naira dubu hamsin a kudin Najeriya.
Daga Kamfanin dillancin labarai na GCLIVES HAUSA
TARE DA WAKILINMU
Auwal M Tukur