Shin, Har Yanzu Ba'a Sami Irin Waɗannan Malamai Bane??






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DOLE ABINDA YA SAMI ANNABAWA YA SAMI MASU YIN KIRA ZUWA ADDININ ALLAH

Idan kana sauraron wa'azozin malaman addinin muslimci na kowanne bangare, wato, Izala, 'Dariqa, Salafiyya ko Shi'ah sai ka ji suna cewa, babu wani Manzo da Allah ya aiko face sai shugabannin zamaninsa sun cutar dashi, kuma jama'a sun qyamace shi.

Kuma suna cewa ita ce hanya wacce babu canji, suna qarawa da cewa , saboda haka duk mutumin da yace zaiyi addinin gaskiya kamar yadda Annabi (S.A.W.W)yazo dashi, to, dole ne sai shi ma an cutar da shi da irin cutarwar da aka yiwa Manzanni (A.S).

Ni kuma duk lokacin da naji wani malami yana yin irin wannan bayani, nakan saurare shi sosai ko zan ji ya bada misali da wani malami a wannan zamani wanda ke fuskantar irin abinda Manzanni suka fuskanta, amma sai naji sun wuce ba tare da kawo misali ba.

Wannan abu na matuqar ban mamaki da kuma daure min kai, har ma na riqa tambayar kaina kamar haka;

DANNA NAN👇
☞ ͡Nine El-Zakzaky, Babban Wanda Aka Fi Zalunta
☞ ͡Yaa Ubangiji! Kurkuku Ne Mafi Soyuwa Daga Abinda Suke Kirana Zuwa Gareshi
☞ ͡Jahili ne Kaɗai, Ke Murna Da Kisan Kiyashin Da Akai Wa Ƴan Shi'a

-Shin, har yanzu ba a sami wani malami daya (1)da ke yin da'awa irin ta Annabawa bane?

-Idan kuma akwai, shin, irin abinda ya sami Annabawa yana faruwa a kansa?

-Idan kuma akwai wanda hakan ke faruwa a kansa, to, me yasa malaman ba sa bamu misali da shi don mu san shine ya gaji Annabawa (A.S)?

-Shin, ko dama ana samun hassada ne daga malaman addini?

-Shin, me yasa masu saurare ba sa yiwa wadannan malamai tambaya kan irin wadannan maganganu nasu?

GASKIYA INA BUQATAR SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI NAWA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~27th April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post