Da sunan Allah mai murkushe azzalumai. Ya ’Yan uwa Musulmi maza da MATA! Assalamu alaikum wa rahamatullah.
An ruwaito cewa Sayyidina Ali Dan Abu Talib (Allah ya yarda da shi) ya ce:
“Ya ku mutane, hakika Manzon Allah ya ce; ‘idan wani ya ga wata gwamnati ta mai da zalunci kiranta, ta keta haddodin Allah, ta shuka kiyayya ga sunnar Manzon Allah, tana aikata barna da zalunci a tsakanin bayin Allah, to a wannan hali duk wani wanda bai yi amfani da hannunsa da bakinsa ya yi yaki da wannan zalunci da barna ba, to ya sani fa Allah zai kai shi matsugunin wannan Jagoran gwamnati, ya sa duk cikar su a wuta.”
To fa! Ga shi kuwa gwamnatin kasar nan ba ma kawai ta mai da zalunci kiranta bane, a kan zalunci ne aka gina ta; ba ma kawai ta keta haddin shari’ar Allah bane, ta aje shari’a ne waje guda ta dauki shari’ar da mutum ya tsara; ba ma kawai ta karya alkawarin Allah bane, tun farko ma ba ta dauki alkawarin Allah din ba! Ta ki ta dau alkawarin Allah, ta yi wa Allah tawaye, amma ta dauki alkawarin Dagutu. Ba ma kawai tana aikata barna da zalunci a tsakanin mu bane, ai ta ma maida wannan zalunci adalci!
Ba shakka mu kuma ba ma kawai mun ki yin amfani da hannuwanmu da bakunanmu don mu yaki wannan zalunci da barna ba ne, ai mu ne da kan mu muka yarda ta aikata wannan barna da zalunci a kan mu! Mu ne fa muka zabi wannan azzalumar gwamnati da hannuwan mu, kuma muke goyon bayan ta da bakunan mu. Kun ga ashe mu ne muka ba shugabannin gwamnati damar su zalunce mu, su kau da shari’ar Allah waje guda, su dauki shari’ar da mutum ya tsara. Mu ne muka ba su damar su aikata barna da zalunci a tsakanin mu, kuma su maida wannan barna da zalunci halal. Ba ma kawai mun ki yin amfani da jikin mu da bakinmu don mu yaki wannan hali ba ne, a maimakon haka, mu ke karfafa mu su gwiwa su ci gaba.
To fa ’yan uwa Musulmi! Idan wannan hadisi ya ce duk wanda ya ga wani shugaba yana zalunci, amma ya ki ya yake shi da ayyukansa da bakinsa, to ya sani fa makomarsa daya da wannan azzalumin Shugaban, to ina ga mu? Kun ga ashe ba ma kawai yana ga Allah na ya dauke mu Ya kai mu mazaunin wadannan azzalumai, Ya sa dukkanmu a wuta ba, ai mu da kanmu ne azzaluman.
E mana! Don me ba zan ce haka ba? Mune fa muka zabi wannan gwamnati, kuma muna jin cewa tamu ce. Mun sa mata suna “Gwamnatin mutane, wadda mutane suka yi, domin mutane.” Kuma muna jin mune mutanen. Da mu da gwamnatin duk abu daya ne. A wannan hali ta yaya za mu iya cewa shugabannin ne kurum azzalumai, amma mu ba ruwanmu? Da mu da shugabannin - shugabannin Kananan Hukumomi, da Gwamnoni da Shugaban kasa duk cikar mu azzalumai ne, kuma duk cikarmu masu laifi ne!
Don me hakan ba zai zamo kashin gaskiyar al’amari ba, alhali Allah Madauki ya tsara, kuma ya kammala, kuma ya saukar mana Alkur’ani mai girma, amma mu muka ki kememe, muka zaba wa kanmu tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya? Tsarin mulki, wanda mutum 50 ba daya suka tsara mana, kuma wakilanmu wadanda muka zaba suka je suka zartar mana? Alhali Allah Ya shirya mana Musulunci (Islam) ya zama hanyar rayuwarmu, amma mu muka ce a’a mu dimakradiyya muke so. Alhali Allah Madaukaki ya zarta da dokar cewa shari’arsa za mu yi amfani da ita, amma muka watsar, muna aiki da dokoki na Turawan Ingilishi! Alhali Allah Madaukaki Ya hore mu da mu nemi gidan lahira, amma muna jin mun gamsu da rayuwar wannan duniya kamar nan ne matabbata. Bilhasali ma don me hakan ba zai zama kashin gaskiya ba, alhali Allah Madaukaki Ya hukunta cewa shi ne kawai za a bautawa, amma mu a maimakon haka kasa muke bautawa.
Ya ’yan uwa Musulmi! Mai yiwuwa ne abin da nake fadi ya yi maku wuyar ganewa, amma wallahi gaskiya nake fadi! Mai yiwuwa ku ga kun kasa yarda, amma a gaskiya a halin yanzu muna zaune a cikin kafirci ne. Musulunci kam babu shi a wannan kasa! Musulunci a wannan wuri sifili ne, a gaskiya ma bai kai sifili ba a nan. Eh mana. Sai dai fa muna da guggubin Musulunci wanda ke cakude da al’adun kakannin mu da kuma tsarin Jahiliyya, wanda Turawan mukin-mallaka suka kawo. Guggubin kuwa ko an tara ba zai zama daidai da komai ba. Misalin Musulunci a wannan kasa kamar jirgin sama ne da ya fado ya kone kurmus. Guggubinsa da suka ragu ba za su yi daidai da jirgi guda ba. Ko kuma ana iya tara guggubin waje guda jirgin ya tashi? To haka Musulunci yake a wannan kasar.
A zamanin da, an taba kafa Musulunci a wannan kasar. Kungiyar masu jihadi a karkashin Shehu Usman Danfodiyo suka kafa shi. Daga baya sai miyagun sarakuna suka fara kaucewa; daga karshe Turawan mulkin-mallaka (wadanda suke tsantsar makiya Allah ne) suka zo suka rushe Musuluncin baki daya. Na’am. Turawa sun rushe Musulunci a wannan kasar suka musanya shi da al’adun gargajiyar su, al’ada ta jahiliyyah. Kuma suka tabbatar cewa sun raini ’yan kanzagin su daga cikin mutanen mu, daga baya suka mika rikon wannan tsari na kafirci da suka kawo a hannun ’yan kanzagin da suka raina suka yaye. A yanzu mu ’ya’ya da jikokin rainon Turawa ne, ga shi a kullu yaumin muna tafiyar da wannan nizami na kafirci, muna rayar da shi.
Hakika muna raye ne a cikin jahiliyyah ta zamani. Muna tafiyar da ita muna tunkuda ta gaba. Kun ga ashe matsayin mu ya fi muni a kan matsayin Musulmi wadanda suka ga zalunci amma suka kyale, suka ki motsi suka yi gum da bakin su. Matsayin mu a yanzu shi ne na Musulmin da suka yarda su zauna a cikin tsari na kafirci. To, me kuke tsammani zai zama makomar mu? Menene zai zama hanzarin mu ga Allah Madaukaki a ranar hisabi?
A bisa abubuwan nan da na ambata, ina yin shela a gaban ku, kuma Allah (Subhanahu wa Ta’ala) shi ne shaida ta cewa, ni dai na kangare wa Tsarin mulkin Nijeriya, da tsarin dokokin ta da shugabannin ta! Ban amince da ko daya daga wadannan ba!! A maimakon haka ina dada tabbatar da imani na ga littafin Allah, da shari’ar sa da kuma shugabancin Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi)!!!
Ba zan zauna ba sai na yi maku bushara. Akwai wani hadisin Manzon Allah (Tsira da Aminci a gare shi) a inda yake cewa:- “A farkon kowane karni Allah zai ta da wani wani da zai jaddada wa wannan al’umma addinin ta.” Kuma alhamdu lillahi kwanan nan muka shiga sabon karni, wato karni na 15. Saboda haka ne ma muka zabi taken wannan taro ya zama a kan karni na 15. Wannan taro shi ne irin sa na 25 da wannan kungiya ta yi. A cikin su biyu ne kawai aka yi a wannan sabon karni. Taken wannan taro na baya shi ne Imani - wato makamin da muke bukata don rusa wancan kafircin. Kuma fatan mu shi ne mu ga bayyanar wannan Mujaddidi wanda Manzon Allah ya gaya mana cewa Allah Ya yi alkawari.
“A bisa abubuwan nan da na ambata, ina yin shela a gaban ku, kuma Allah (Subhanahu wa Ta’ala) shi ne shaida ta cewa, ni dai na kangare wa Tsarin mulkin Nijeriya, da tsarin dokokin ta da shugabannin ta! Ban amince da ko daya daga wadannan ba!!
A maimakon haka ina dada tabbatar da imani na ga littafin Allah, da shari’ar sa da kuma shugabancin Manzon Allah (Tsira da Aminci a gare shi da iyalan gidansa)!!!”
Tags:
Jagoran Gaskiya