Sayyid Zakzaky (H) ne aka zalunta, bashi yayi zalunci ba balle a yafe masa!





Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Gen. Buhari bama buƙatar afuwar ka, Afuwar ka, bazata ƙarama malam zakzaky matsayi wajen Allah ba, rashin afuwar ka bazata ragema malam matsayi wajen Allah ba, malam ga Allah ya dogara, kuma hukuncin Allah yake jira a tsakanin sa da ku.

Zama gidan kaso, ibada ce babba a wajen Annabawa da manzanni, dakuma bayin Allah na gari, Buhari daba jahili bane kai da nace kabinciki tarihin magabata, to matsalar kai jahili ne.

Bari infaɗi akaranta maka, kuma zanfara da misalin mutane masu gwagwarmayar neman 'yanci, irinsu Nelson Mandela.

Wanda ya sadaukar da rayuwansa wajen samar da yancin kai na al’ummanr kasarsa. Nelson Mandela abin kwatance ne ga dukkanin wani mutum mai bukatar ’yanci a rayuwarsa.

 Nelson Mandela ba gwagwarmaya ya yi a kwance ba, ya mike tsaye ne ya sha wahala sosai wajen neman yancin kan al’umman kasar shi.

Ya yi gwagwarmaya ya sha dauri da wahalar zaman gidan yari da muzgunawa da daukar kaskanci daga bisani ya yi nasara.

Nelson Mandela, ya samu nasara da daukaka yau al’umma su na tunawa da rayuwarsa ba a kasarsa kadai ba, Duniya bakidaya ta na tunawa da kokarinsa da sadaukarwar da ya yi.

Har takai munajin cewa kowannen mu yana ji cewa zai iya zama Nelson Mandela wajen samar da ’yanci da zaman lafiya.

Saboda Mandela mutum ne mai bukatar son zaman lafiya cikin Duniya ga kowace al’umma.

Cikin koyarwansa akwai kyawawan abin koyi wanda Duniya take karuwa da shi. Saboda yadda bai fifita kansa ko iyalansa a kan na kasa da shi ba.

Rayuwarsa rayuwa ce mai cike da farin ciki da tausayi da ma taimakawa al’umma. Hakan ya sanya duniya ke bikin tunawa dashi a duk 18 ga watan bakwai 7 na ko wace shekara.

Nelson Mandela takaiga duk wani musulmin duniya yanaji dama nasu ne, (musulmi).

Idan najuya baya, Gen. Buhari kasanya a karanta maka tarihin rayuwar Annabin Allah Yusufu(A.S) tsoron Allahn sa gaskiyan sa da riƙon amanar sa da kaucewa ɓarna(Alfasha) yasanya aka garƙameshi gidan yari ba laifi yayi ba. Annabi yusuf A.S bai taɓa nadama ba Annabi yusuf baitaɓa danasanin zaman sa gidan yari ba.

Hasali ma yafi jin daɗin rayuwa agidan yarin bisa ga gidan sarauta saboda zama gidan yarin Ibada ne babba. Kuma akullum addu'a yake ma al'umma da neman shiriya, yana tsare ƙasa ta fuskanci matsala daga cikin gidan yarin yabada shawara da mafita kuma akayi amfani da shawara aka samu mafita, kaji cikakken imani.

( Inama wan'nan Gwmnatin zata sauke girman kai koda ta ƙarƙashi ƙasa ne sunemi shawara kan halin da ƙasar nan take ciki nayi imani, wallahi da malam zakzaky yabasu ingantacciyar shawara da kuma zata zama mafita) wan'nan shine cikakken imani da 'yan'adamtaka.

Na tsakuro maka rayuwar Annabi yusuf ne, saboda ƙila kai musulmi ne, inkuma ba shi bane ga rayuwar Nelson Mandela nan.

Kuma atarihi babu wani ɗan adam mai fafutukar neman 'yanci da aka taɓa yin galaba akan sa sai dai shi yayi galaba, ko anyi nasarar kashe shi to ƙarshe tawaye da bore ke biyo baya wanda yake sabbaba kifar da Gwamnati idan baka sani ba kasanya abincika maka.

Kamar yanda na faɗi abaya malam Zakzaky ku kuka zalince shi, kuma kuke cikin zaluntar sa. Tsa6won shekara arba'in malam yana da'awa da shelanta, baya tare da Azzalumai, sukuma shuwagabannin Nigeriya mafi yawa Azzalumai ne don haka malam zakzaky bashi da Abokin aminci acikin su.

KARANTA WANNAN👇 
Imam Mahadi (Ajtfs) Fita Na Biyar (5)
Non Communicable Diseases Part (1)
Covid-19 da Gwamnatin Nijeriya – Nazari


Malam Zakzaky yayi tawaye ga Zalunci yace shi musulmi ne, kuma musulinci za'yayi, yayi bara'a wa Gwamnatin kafurci. Ina so don girman Allah asamu wani malami masanin addini komin girmansa komin ilimin sa, intambaye shi, "shin ita wan'nan Gwamnatin da ke jagorantar ƙasar nan a ƙarƙashin mulkin Gen. Buhari shin, Gwmnatin musulinci ce?

Idan amsa itace 'a'a' to kai musulmi da kake da littafin Allah al'qur'ani kuma al'qur'anin nan yayi hannun riga da tsarin dokokin ƙasa. Kuma shi, Al'qur'anin aka wajabta maka kabi idan kabi zaka shiga Aljanna idan ka bijire zaka shiga wuta, kuma umarni daga bakin manzon Allah, to miye laifin ka don kace ka fanɗare ma tsarin kafurci na Allah zakabi?

Malam Zakzaky Allah ya haska masa haka azuciyar sa, kuma ya baiyana a zahiri bai ɓoye ba, kuma yakeyi a aikace, shiyasa ma Gwmnatin tsarin kafurci take faɗa dashi.

Duk'mai bin koyarwar gidan Annabi ta haƙiƙa to baya zalunci kuma baya bari a zalunce shi, "ma'ana ba'a zaluntar sa yayi shiru" Shiyasanya malam Zakzaky yake yaƙi da zalunci da Azzalumai, da ɗumbin ilimin da Allah ya hore masa da kuma fahimtar sa.

Wan'nan fahimtar kuwa itace irin ta Annabi yusuf Itace irin fahimtar Annabi Musa Itace irin fahimtar Annabi Isah, Itace Irin fahimtar Annbai Muhammadu s.a.w.w, dama sauran Annabawa, babu wanda yayi tarayya acikin zalunci.

Kowa ya sani hatta makaho kurma yalaluba ƙasar mu Nigeriya yasan zalunci ke mulkar kasar nan, don Allah malamai kudaure kuma kuyi bara'a wa zalunci kuce bakwa goyon bayan kafurci, kuma kufaɗa da ikhlasi, kuga abinda zai sameku!

Wallahi irin abinda yasamu Nelson mandela shi zai same ku, wallahi irin abinda yasamu Annabawa da manzanni shi zai sameku, wallahi irin abinda akaima malam zakzaky shi za'aimaku.

Idan kuwa haka ne Ashe malam Zakzaky shine malami masanin 'yanci maƙiyin zalunci, mai neman 'yantar da 'yan kasa daga cikin duhun zalunci, Ashe malam Zakzaky shine Nelson Mandela na wan'nan zamanin shine Yusufu zaman.

MALAM ZAKZAKY-Shine wanda yashekara arba'in ana kawo masa hujumi ana neman makasar sa, Malam zakzaky shine wanda ya shekara arba'in cikin ƙunci da zama gidajen yari daban daban.

MALAM ZAKZAKY- Shine wanda aka kashema 'ya'ya shida da dangin sa aka kuma kashemasa Al'majiran sa sama da dubu aka harbeshi shida matar sa aka jashi cikin jini akaje ka kulle tsawon shekara hudu ba magani ba belin.

MALAM ZAKZAKY-Shine wanda aka rusama duk wani abu da ya mallaka aka share ko kufai ba'abari ba. Amma babu abinda yace sai" Kuyi haƙuri haka hanyar take"

Wan'nan wane irin mutum ne mai son zaman lafiya alokacin da yake da matasan da suke neman mutuwa ido rufe, suke jiran umarni sa, atafasa uban kowa ya ƙone! Amma duk da haka yakecewa, mu lahira ce a gaban mu, ba wan'nan tarkacen duniyar ba, idan mulki muke so tubalin toka yafi wan'nan Gwmnatin saukin rugujewa, amma mu Al'umace gaban mu.

Wan'nan bawon Allah shine abin ƙi ga daƙiƙan mutane, shine abin kisa abin daurewa.

Lallai inakira ga duk'wani ɗan Nigeriya mai irin halin Gwamnatin Nigeria da ya gaggauta neman gafarar Malam Zakzaky.

Malam Zakzaky zinari ne a wan'nan zamanin neman irin sa ake saboda ƙalilan ne aduniya.

Wasalamu alaikum. IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post