Saɓanin ganin watan Ramadana ko Shawwal






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AMSA DAGA FATAWAR SAYYID KHAMENE'I

Wannan amsa tazo daidai da wannan zamani wanda aka mayar da al'amarin ganin wata bin son zuciya.

Kar dai na cika ku da surutu, ku biyo ni.

TAMBAYA :- Idan aka sami sabanin malaman wani gari dangane da ganin wata da kuma rashin ganinsa, kuma adalcin wadannan malamai dukkansu ya tabbata ga mutum, kuma yana da yaqini kan bincike da bin diddigin kowanne daya daga cikinsu, to, menene ya wajaba ya aikata?

AMSA :- Idan har wannan sabani nasu kan korewa ne da kuma tabbatarwa (da ganin watan)kamar wasunsu suyi da'awar tabbatar watan, wasu kuma suyi da'awar tabbatar da rashi tsayuwarsa, to, hakan karo ne tsakanin hujjoji biyu. To, a wannan hali sai mutum ya jefar da dukkan wadannan maganganu biyu, ya koma yayi riqo da abinda shari'a ta tabbatar na yin aiki da asali daga usul, wato kamar babu wadannan maganganu.

DUBA NAN:
☞ ͡Iyali A Muslunci... Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa Ni Part (3)
☞ ͡Wannan Harkar tana koyar damu riƙon amana ne!

To, amma da ace sabanin nasu ya ta'allaqa ne da tabbarwa da kuma rashin masaniya kan tabbatuwan, kamar wasunsu suyi da'awar ganinsa, wasu kuma suce su basu ganshi ba, to, maganar wadanda suka ce sun gani idan dai adalai ne shine abin riqo a shari'ance ga mutum, kuma wajibi ne ya bi hakan. Haka kuma da Marja'i ko kuma Waliyul Faqih zai bayar da sanarwar ganin watan, to, hukuncinsa hujja ce ga dukkan mutane, kuma wajibi ne su bi shi.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~22nd April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post