Nazari akan zaman aure Part (3)





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Suhaila Aminu Sidi


Haquri shine jagoran warware kowace matsala. Miji zai iya fuskantar wasu qananun matsaloli a cikin gida, kamar gishiri yayi yawa a cikin abinci. Wanda baya iya jure hakan.

Aikinka shine kayi qoqarin fuskantar da matarka wannan matsalar cikin hikima, maimakon ka maida gidan naka filin yaqi.

Ya kamata miji ya kalli wannan matar shin abu nawa ta sadaukar saboda shi? Shekaru nawa tayi tare dashi ? Qilama gashinta yayi fari tana gidanshi wajen shirya maka abinci da kula da yaranka, bata cancanci wulaqantawa ba a lokacin da zakai mata hukunci

💟💟💟💟💟💟💟💟💟

KARANTA WANNAN👇 
Imam Mahadi (Ajtfs) Fita Na Biyar (5)
Non Communicable Diseases Part (1)
Covid-19 da Gwamnatin Nijeriya – Nazari

Wasu mazajen suna bibiyar matarsu a cikin kowane qaramin abu daya shafi rayuwarsu, hatta yanda take numfashi, da irin kayan da take sawa, da irin cin abincinta. Suna so dole sai tayi yanda suke so.

Suna neman ta basu abunda ba haqqinsu ba.

Na'am yana da haqqin ya tuhumeta akan abubuwan da shari'a ta bashi dama, kamar Almubazzaranci da kayan da shari'a ta haramta.

Bawai ya sa mata ido a bisa al'amurran al'ada ba. Domin yawan tuhuma da tsegumi yana raba tsakanin masoya da abokai. Kuma za'a iya kaiwa matakin da tsegumin bazaiyi tasiri akan matar ba. Kaga mutumcinka ya zube kenan. Sai a kiyaye.

Mace tana tsananin son namijin dazai fahimce ta, ya girmama abunda take so, baya yimata izgili. Dayawan mata zaka ji suna cewa: (Ni babu wanda yake fahimta ta).

Cigaba.... KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post