Tare da Suhaila Aminu Sidi.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Ya kai Mai gida... Ka jinkirta abunda kake so ka gyarawa matarka harsai kunzo lokacin da kuke haduwar soyayya, a wajen tattaunawarku.
Hakan zai kubutar dakai daga dukkan wani mummunan zato da zatai maka. Sannan a wannan lokacin bazata iya bijirewa dukkan abunda kazo mata dashi ba.
Mace halittace mai sauqi..ta hanyar magana mai dadi zaka iya sayeta..kawai ka karramata, ka girmamata, ka kula da ita, zaka samu abunda kake so.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Ku sabawa kanku da rashin taurin kai.
Taurin kai shine fetur din dukkan wata mushkila.. Zai iya yiwuwa matsalar sassauqa ce, amma sakamakon taurin kai ta koma babba, ta hargitsa rayuwarku.
KU KARANTA NAN 👇
☞ ͡Da Ɗumi-Ɗumi: Yaron gwamna Nasir El-Rufa'i yayi wa wani ɗan Ƙabilar Igbo Barazanar yiwa Mahaifiyar sa Fyaɗe
☞ ͡Kayi abinda ƴan Nijeriya zasu riƙa tunawa dakai bayan kabar mulki – Sakon Gwamnan Sokoto Ga Shugaba Buhari
☞ ͡Sojojin India da Pakistan sunyi musayar wuta a yankin Kashmir, Mutum biyu sun rasa ran su
Zai iya yiwuwa matsalar zata warware ne kawai idan dayansu yace : (Nayi kuskure kuma ina neman afuwa) amma sakamakon taurin kai sai wannan jumlar tayi wahala kamar za'a mutu in aka fadeta.
Tabbas indai taurin kai ya cigaba, to gidan dayake cike da farin ciki zai iya komawa 'yar qaramar kurkuku ga ma'abotansa, ta yanda kowa kanshi ya sani, dukkan wanda ba shiba to qarqashinshi yake. Wanda hakan matsala ne.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Akwai banbanci tsakanin Gaskiya, da kuma Fahimtar gaskiya.
Zai iya yiwuwa miji yana da gaskiya, amma bai yima matarshi bayani yanda zata gane ba.
Mutum zai iya samun sabani da matarshi, sai yai qoqarin tursasa mayarshi akan wani ra'ayi nashi, wanda bata fahimta ba..ko kuma bata yarda dashi ba dukda gaskiya ne.
Ba haqqinka bane ka dauka cewa komai naka dole sai an yarda dashi..amma muna kira ga miji ya samu cikakkiyar qwarewa wajen fahimtar da matarshi dukkan matakin daya dauka a rayuwar aurensu. Hakan zai taimaka wajen magance matsaloli.
Cigaba....
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar Ma'aurata