Nazari akan rayuwar Aure Fita Na Daya (1)




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Suhaila aminu sidi✍

Warwarar matsaloli suna farawa ne tun kafin faruwar matsalar, a yayin da miji zai bude zuciyar iyalinshi.

Sanannen abune dukkan wanda yake so ya canza zuciyar wani kuma yake so ya fuskantar da ita zuwa abunda yake so , to dole saiya fara shiga ta hanyar soyayya da tausayi da kyautatawa.

Wanda wannan ginin soyayyar zai zama babbar katanga a matakin farko wacce babu matsalar da zata iya girgiza ta. Kai kodama an samu girgizar to baza tayi barna sosai ba.

Lallai mace tana son kulawar mijinta a kowane lokaci, da kyautar bazata...tana son miji wanda yasan rayuwa.

Kuyi magana da matanku da sassauqan harshe, domin a cikin zuciyar mace akwai wani fulawa, tana girma ne tayi kyau a yayin da aka shayar da ita daga ruwan soyayya da tausayi da kulawa.

Kyakkyawar magana kamar kogine mai sanyi, kuma mai dadi wanda yake kashe Qishin zuciya.

Haquri shine jagoran warware kowace matsala. Miji zai iya fuskantar wasu qananun matsaloli a cikin gida, kamar gishiri yayi yawa a cikin abinci. Wanda baya iya jure hakan.

Aikinka shine kayi qoqarin fuskantar da matarka wannan matsalar cikin hikima, maimakon ka maida gidan naka filin yaqi.

Ya kamata miji ya kalli wannan matar shin abu nawa ta sadaukar saboda shi? Shekaru nawa tayi tare dashi ? Qilama gashinta yayi fari tana gidanshi wajen shirya maka abinci da kula da yaranka, bata cancanci wulaqantawa ba a lokacin da zakai mata hukunci.

Cigaba.... IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post