Nazari akan Rayuwar Aure Fita Na Biyu (2)





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Suhaila aminu sidi✍

Taurin kai , da zafin magana , da hayaniya basu amfanarwa da komai a yayin da ake so a fuskanci mushkila.

Kuyi qoqarin fahimtar juna ta hanyar tattaunawa cikin wayewa, ta yanda Nutsuwa da girmamawa zasu jagoranci tattaunawar.

Duk mutumin da yake so ya kiyaye farin cikin iyalinshi to dole yayi imani da tattaunawa da mutumtawa, sannan ya kiyaye sharuddan addini da ilimi a yayin tattaunawar.

Bazai yiwu ace wannan auren anci ribarshi ko akasin haka ba harsai an samu riqo da juna da tabbatuwa.. Misalin afuwa da kauda kai...waye a cikinmu baya kuskure? Annabi yana cewa :(Dukkan 'yan Adam masu kuskure ne, amma mafi alkhairin masu kuskure sune masu tuba)/

Ma'aurata suna iya daukarwa kansu cewa zasu warware dukkan wasu matsaloli ta hanyar tattaunawa da sanya zurfin tunani da fahimtar juna.


Kowace matsala ce a rayuwa ana iya warwareta ta hanyar Tattaunawa da sanya tunani. Shikam taurin kai, da jayayya yana tasowa ne daga wanda baya da gaskiya a mafi yawan lokutan.

Zata iya yiwuwa miji yana cikin irin wadannan mutanen da suke tursasawa matarshi ra'ayinsa ko bata so, bisa taqamar shine jagoran gida. Wannan kuma kuskure ne babba. Domin hakan zata iya kaiku ga rashin fahimta , daga nan sai matsaloli daganan sai saki (Allah ya tsare). 

Amma mace kana iya sanya mata ra'ayinka ta hanya mai sauqi da magana ba hayaniya ba.

Cigaba...


IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post