Namiji Yafi Buƙatar A Bawa Kulawa Fiye Da Mace!





Rbtw: Yaseerah Baseeru Shee'it

Duk da yake Ni mace ce, amman hakan bazai hanani nayi adalci cikin rubutu na ba.

Sau dayawa muna cewa maza suna da tsaurin zuciya, ma'ana bushashiyar zuciya, (قسوة القلب) ta kafe wa akan abu, Mu kuma muna ɗaukar kanmu masu tattausar su zuciya.

To idan muyi tambaya ne, waye yafi buƙatar kulawa tsakanin mai taurin zuciya da kuma mai lallausar zuciya?

Nasan kowa zai ce ganda abawa mai tsaurin kulawa' wanda kuma a gaske hakan ne yakamata, tunda ƙila silar hakan ne zaisa yasamu nutsuwa"

Wanda yake fin yawan shan wahala da kuma faɗawa haɗura' lalle shine wanda yafi abawa kulawa, don da kulawar ne kaɗai za'aja zuciyar sa.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Bawai nace mace bata bukatar kulawa bane itama!!! Sai dai namiji Yakamata Afi bawa, tunda shine yake yin aure da tunanin zai samu kulawa.

Ita mace ba kulawa tafi soba' tafi son kariya (الحماية) duk dayake ko wacce mace akwai abinda take ganin shine zai bata kulawa.

Wata tana ganin na miji mai kuɗi shine yafi mata' saboda kuɗi take tunanin zai sama mata kariya.

Lokacin da wata kuma ta zaɓi mai ilimi saboda a gurin ta ilimi ne zai bata kariya.

Wata kuma ɗan dambe zakaga yafi burge ta, saboda a gurin ta, da ƙarfi ake bada kariya.

Hakan ne yasa zakaga ko wacce mace akwai kalar namijin daya fi burgeta, wanda wata ƙila wata hakan bai burgeta.

Idan muka saka nazari da kula sosai, lalle zamu fahimci' cewar namiji ya cancanci abawa kulawa sosai.

Amman abin takaici mu yanzu mata, munfi damuwa' da son zuciyar mu, wanda kuma a gaskiya Hakan kuskure ne.

Sau dayawa idan mazajen mu suka ɓata ransu, mai makon mu rarrashe su sai muma muce zamu ɓata ran mu, dan abamu kulawa.

Lokacin da mijin ki ransa' ya ɓaci to kada ki gajiya wajan bashi haƙuri, haɗi da lallashi, koda kuwa zaina cin mutuncin ki, ki daure, kisawa zuciyar ki' kin daure ne don misalta umarnin Allah bawai dan. Wani abun ba.

Fatana zamuyi nazari don mu gyara mu'amalar mu da abokan zaman mu, mu basu kulawa koda zamu sha wahala.

LADAN MU YANA GURIN ALLAH.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post