Me yasa yanzu maza suka fi mata tsada a wannan zamanin?





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

IDAN KANA DA KUDI ZA KA SAMI MATA A QANQANIN LOKACI

Anyi wani zamani a baya na qarancin mata yadda za ka tarar yarinya (Budurwa)na da samari 5 a lokaci guda saboda qarancinsu, kuma kowanne daga cikinsu neman aure yake yi mata.

A wannan zamanin kuwa in har kaga budurwa na da samari 3, to, 2 daga cikinsu mayaudara ne ko ma dukka 3. Kuma ba za a gane hakan ba har sai anyi musu umarni da su fito don a basu auren.

Matan zamanin baya ba sa yin bandaro komai muninsu da jahilcinsu, amma na wannan zamani sai ka tarar ga kyau (beauty), ga kyan siffa (shape/body), ga ilimi na zamani dana addini, amma kuma a qa'ida sai kaga kamar ma sun wuce lokacin da za ka kira su da sunan 'yanmata, sun fi dacewa da zaurawa ko matan aure, amma kuma babu mijin auren.

Amma a hakan sai ka tarar wasu daga cikinsu don rashin hankali, tunani, da rashin sanin mutuncin kansu, sun zami wanda ya nuna yana sonsu amma kuma su wanda suke hange nanan daban wanda shi ba sune a gabansa ba.

LATSA NAN 👇
☞ ͡Da Ɗumi-Ɗumi| Yaron Gwamna Malam Nasir El-Rufa'i yayi barazanar yiwa mahifiyar wani ɗan ƙabilar Igbo Fyaɗe
☞ ͡Ina wanda bashi yayi mar yawa, har ya kasa biya. To, gawata addu'a kamar yankan wuƙa
☞ ͡Wake neman kariya daga sharrin Shaidan (L.A)?
Coronavirus| An kama mutanen da suka daurin aure a wani masallaci

Sai dai a hakan akan sami masu hankali daga cikinsu wadanda matuqar sun sami wanda ya nuna yana sonsu da gaske, to, sukan riqe shi da qarfi(firmly)don kada ya kubuce musu.

     MATSALAR NAMIJI

Shi namiji babbar matsalarsa kawai ita ce rashin kudi, amma in yana da kudi mace ba za tayi masa wuyar samu ba.

Dalili kuwa shine, idan aka ce ya je wajen wannan (mace)ta nuna ba ta sonsa, to, akwai 70 kamarta na nan suna jiran samun irinsa.

Saboda hakane ma za ka tarar da wuya ace namiji ya kai wani lokaci wanda za ace lokacin yin aurensa ya wuce, amma mata sai dai ayi sha'ani. Domin su kan kai wani lokaci da aurensu ma yakan zama lalura ce don rufa musu asiri, amma aurensu sai an rintse ido !

DAMARKI CE YARINYA, KAR KI YARDA TA KUBUCE MIKI !

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

09039791509-08126385470

~14th April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post