MACE A MA'AUNIN HANKALI DA ADDINI
abbagano
(Tattaunawata da wani dan'uwa )).
__________________________________
__________________________________
★SAUKEWA MACE NAUYIN IBADU A LOKACIN HAIDHA KARRAMAWA CE DA TAUSAYAWA DAGA ALLAH★
Bisa dabi'a ta addini da Shari'a to Allah yana tausayawa raunana da marasa lafiya, shiyasa zakaga da yawan TAKLIFI idan yazo akansu sai ace ya fadi, kuma wannan ba naqasu bane , domin shiya fadi cewa : Baya dorawa rai sai abunda take iyawa. kuma wannan ba Naqasu bane, yana nuna tsantsar tausayin ubangiji ne ga bayinsa.
A iya litattafan dana karanta game da sanin halayyar dan Adam , musamman wanda suka shafi Mata kamar :
١ - ﺩﻧﻴﺎ ﺍﻟﻔﺘﻴﺎﺕ ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻘﺎﺕ
٢ - ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺍﻃﺮﺍﺑﺎﺗﻬﺎ ﺍﻟﻨﻔﺴﻴﺔ ﻭﺍﻟﻌﻘﻠﻴﺔ
٣ - ﻣﺎ ﻻ ﻳﺪﺭﻛﻪ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﺗﺤﺘﺎﺝ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
٤ - ﻣﺎﺫﺍ ﻳﺴﺄﻝ ﻋﻨﻪ ﺍﻟﻔﺘﻴﺎﺕ .
MASU ALAƘA:
◉Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani Part 3
◉Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani Part 4
◉Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani Part 5
◉Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani Part 6
dadai sauransu. tona lura cewa suna jinjinawa idan sukazo magana akan abunda ya shafi al'ada ta mata, Abunda sukafi karfafawa akanshi shine :
1- Dayawan nauyi da ayyuka yakamata a daina dorawa mace idan tana wannan hali
2- Rashin daukar mataki akan laifin da tayi a wannan hali (domin zai iya yiwuwa ba'a son ranta tayi ba).
Banyi mamaki ba a lokacin danaga Musulunci yana karfafa wannan zantuka yana cewa:
1- An daukewa mace ibadu kamar sallah da azumi da sauransu harsai ta fita daga wannan yanayi.
2- Bai halasta ga mijinta ya saketa ba a wannan hali.
3- Bai halasta mijinta ba ya kusanceta a wannan hali.
Dadai sauran hukunce hukunce da suke nuna tausayawar Musulunci ga macenda ta samu kanta a wannan yanayi.
Yauda ace wani zunubi suka aikata aka horasu da wannan rashin lafiya, da sai kace naqasu ne. Amma Babu inda Allah ya nuna hakan.
Saboda haka gaskiyar magana Al'ada ga mace ba naqasu bane a cikin addininta, kai shinema cikar addinin nata. tunda idan ta shiga wannan yanayi akwai dokokin da akan sanya mata idan ta kiyayesu tayi biyayya ga Allah, kuma tayi addini kamar rashin yin Sallah a wannan Hali shine addininta.