SHAFI DOMIN KAI DA AL'UMMAR KA!
Abbagano
(Tattaunawata da wani dan uwa)
__________________________________
2- Idan karancin hankali ne zai sanya mace biyu ta bayar da shaida a matsayin namiji daya, to a wurin rabon gado kuma fa?? Shikuma karancin kasanewarta diyar babanta ne yasa take karbar rabin kason namiji?? koko karancin menene ya jawo hakan??
3- Idan har mata masu karancin hankaline, to bai kamata kuce sune mafi yawa a wuta ba, domin Hankali shine hujjar Allah akan bayinsa, Shiyasa ma idan hankali ya fita sai TAKLIFI ya fadi, to idan aikin da mata suke aikatawa na ba daidai ba ya zama daga karancin hankalinsu ne, shin ya dace Allah ya konasu kuwa?? shin bazasu tambayi ubangiji ba cewa : Miyasa baka yimu masu cikakken hankali ba, domin mu gane cikakken sakonka domin mu bauta maka ba?? kuma tayaya zaka tabbatarman da Adalcin Allah idan har yazama zai hukunta mutum akan aikin dayayi saboda karancin hankali??
LATSA NAN: Makircin kashe Sayyid Zakzaky da sunan Coronavirus a gidan yarin Kaduna
4- Tayaya mai karancin Hankali take iya yaudarar Namiji mai cikakken Hankali?? Anya mahaukaci zai iya yaudarar mai hankali kuwa?? Ai idan mutum bayada cikakken hankali bazai taba tunanin yayi yaudara ba, ballantana tayi tasiri. Toba kunce mana Mata makirai bane?? to ku gayamani da karancin hankalin suke makircin??
5- Tayaya mace mai karancin hankali ta raini mutum tun yana cikin cikinta, harya girma , harya zama mai cikakken hankali?? Shin akwai wanda zai yarda acewa mahaifiyarshi mai karancin hankali?? Alhali ya samu nashi hankalin ne daga nata??.
6- Daga karshe niban ce babu mata masu karancin hankali ba, ammadai ba dukkansu ba, domin munga annabi (saww) yana karbar shawara daga Ummu salma (as) , ka duba misalin Ranar Hudaibiyya mana.
Mu hadu a rubutu na 7