Masoyan Zamani Part (1)







Fatima ibrahim✍

Bisimillahi rahamanir rahim

Da farko zanso nayi magana ne akan masoya Amman na zamanin da muke ciki, wanda silar zamanin ne zakaga ƴar malam da ciki ko malam da matar wani!!!

Bawai inna nufin wani abune masoyan zamani sukai ba, a'a zan ɗan kawo hasahe nane kan wannan lamari, wanda nasan ƙila na iya hasasho gaskiya ko akasin hakan.

Zan ɗauki ɓangare ɓangare donyi bayani daidai gwargwado, ko Allah zaisa mu fahimta, tunda a ƙarshe zan kawo hanyar magan ce matsalar

*SAMARIN ZAMANI!!!*

Tabbas nasan yadda zamanin mu yazama abinda yazama, kowa zai iya samun damar yin magana akai' tunda abubuwan a bayyane suke bawai a ɓoye ba!!!

A wannan zamanin zakaga saurayi bai da nufin aure, Amman sai kagan shi da ƴan mata sama da 6 kuma duk shi kaɗai!!!

A duk cikin ƴan matan nasa babu wacce yakejin zai aure ta, Amman a hakan ya dage kullum sai ya kirawo su ko ya taka ƙafa yatafi gunsu.

Na taɓa magana da wani namiji daga cikin ƴan ajin mu, a makarantar mu!!! Nace:-
 mai yasa akasarin ƴan maza na yanzu basu tsaiwa da budurwa ɗaya!!!?

Sai yayi dariya yace nasan sanda akai mana wani tashbihi cikin (balaga) kina nan ko nace wanne ? Yace tashbihin dumni!! Nace inna nan' yace yauwa zaki fi gane wa!!!

Yace yanzu idan kika tsaya da ƙafa ɗaya sai aka zo aka ƙwashe ki, kinga da wuri zaki faɗi ko? Nace ƙwarai kuwa!!!

Yace amman idan ƙafa biyu kika tsaya dasu fa!!? Sai nace ƙila bazan faɗi da gaggawa ba!!! Sai yace to wannan shine banbancin yin budurwa biyu da ɗaya' sai nayi dariya nace kaga kana Iyayi dayawa ma, kenan yadda zaka zama gizo gizo mai kafofi dayawa!!!

Sai mukai dariya muka bar maganar!!!

Tunda Ni ba namiji bace, shiyasa nakawo muku ɗaya daga cikin dalilan da naji masoya maza na zamanin nan suke anfani dashi don yaudara!!!

Bawai labari zan baku ba, kawai zanyi anfani da hujjar danaji daga ɗaya daga namiji, don yin. Warwara ga masu irin wannan tunani!!!

Kada kuyi tunanin bazan magana kan yaudara da sunan soyaiya da ƴan uwana mata muke ba.
 zanso kuyi haƙurin bibiyata!!! Don nabi abin cikin tsari ne:

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post