Masoya Buhari, tamkar masoyan Fir'auna ne a zamanin sa!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KU KARANTA WANNAN QISSA ZA KU FAHINCI HAKA

Tarihi yakan maimaita kansa a lokuta da dama, amma dai masu hankali kadai ke fahinta.

Allah (T)ya kawo mana qissar mutanen Fir'auna da suka qaryata gaskiya da kuma sakamakon wannan qaryatawar.

Ga shi kamar haka:-

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ KUMA HAQIQA GARGADI YA JEWA MUTANEN FIR'AUNA .‘’ Cewa su bi Musa (A.S)don su tsira.

SUN QARYATA GAME DA AYOYINMU (Na manzanci da mu'ujizozi), SAI MUKA KAMA SU (ta hanyar halakarwa a ruwa)IRIN KAMUN MABUWAYI MAI IKON YI .

SHIN, KAFIRANKU (Fir'auna da Hamana)NE MAFI ALHERI DAGA WADANCAN (Manzanni Musa da Haruna), KO KUMA DAI KUNA DA WATA BARA'A (Shaidar samun kubuta)A CIKIN LITTATTAFAI ?

KO ZA SU CE, ‘’ MU DUKA (mabiya da shugabanninmu)MASU HADA QARFI NE DOMIN CIN NASARA?‘’

DANNA NAN: 
Hikima kayan mumini Part 2
Yahudu sun cimma manufar su 80% da wannan cutar ta Coronavirus

ZA A KARYA TARON (nasu na kafirci da zalunci), KUMA SU JUYA BAYA DOMIN GUDU .‘’

  (Suratul-Qamar, aya ta 41-45)

Kuma wannan shine abinda ya faru, domin an halakar da su, kuma sauran kafirai azzalumai irinsu sun guda, domin hada qarfin nasu bai amfanar da su ba.

Yaqin Badr ya zama babban abin misali.

To, idan ka kalli masoya Buhari za ka gansu tamkar mabiya Fir'auna, domin ayoyi daban-dabam na bayyana a gare su game da al'amarin Sayyid (H), amma ba sa daukar darasi saboda shaqaawa (rashin rabo).

Da sannu irin makomar Fir'auna da mabiyansa ne za ta kasance a kansu insha Allah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~3rd April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post