Maƙiyan Ka Suyi Maka Dariya, Kuma Ka Basu Abinci, Wannan Sai Sayyid Zakzaky








Abbagano✍

Ɗazu da yamma nake ganin yanda Sayyid Ibrahim zakzaky ya tura da kayan abinci don arabawa al'ummar musulmi.

Shekaru huɗu kenan da kama shi, amman ko wacce shekara da azumi saiya turo an rabawa mutane kayan azumi.

To wannan shekarar ma kamar sauran shekaru, yasake bada umarnin arabawa al'ummar musulmi abincin AZumi.

Sayyid sun bada umarnin arabawa mutanen gyallesu kayan abincin AZumi wanda yasaba basu duk shekara.

Idan baku manta ba, wasu daga mutanen gyallesu ne suka dinga kwashe kayan gidan sa, lokacin da azzalumai suka afkawa gidan sa da nufin kashe shi.

Bayan ankashe ɗin bin mabiyan sa, haka wasu daga mutanen anguwar suka dinga wawason kaya da kuɗaɗen bayin Allah.

DANNA NAN👇
☞ ͡Ahkham: Hukuncin  Masu Zama Da Janaba Da Gangan.. Futa Na Ɗaya (1)
☞ ͡Shekaru Sha Huɗu Masu Albarka
☞ ͡Nice Suhaila Ibraheem Zakzaky, Wa zai Tausaya Min??


Jikin gawa zasu zo su murginar da ita su kwashe kuɗin jikin su, wasu kuma wuƙa zasu sa suyanke hannu don ciren zobe wasuma takalman su suke kwashe wa.

Sannan duk wani kayan anfani na gidan su Sayyid saida wasu daga mutanen anguwar gyallesu suka kwashe, harda tukunya ta girki.

Lokacin da ake kashe mu sune suke nuna inda wasu ƴan uwan suke, sune suke tsalle da shewa saboda an kashe Sayyid zakzaky.

Amman duk da wannan abinda wasu daga mutanen gyallesu sukai, haka Sayyid zakzaky yake bada umarni duk shekara a kai musu abinci da AZumi.

Sayyid zakzaky ya tuna min da su Imam Ali, a wajan haɗiye fushi.

Allah yakare mana kai magajin Annabawa.

Ga ƙàrin wasu Hotunan👇


KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post