A wani bayani da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta fitar ta bayyana cewa; ci gaba da kai wa Syria hari da HKI ta ke yi, kai wa dukkanin al’umma hari ne domin lalata karfin da ta ke da shi.
(ROHOTON ABNA24.com) Mai Magana da yawun kungiyar gwagwarmayar musuluncin ta Hamas, Hazim Qassim, ya fadawa kamfanin dillancin labarun; “Iran” na Iran cewa; Ya zama wajibi ga al’umma da ta hada karfi da karfe wuri daya domin fuksantar wuce gona da irin ‘yan sahayoniya da taka musu birki.
A nata gefen, kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta “Popular Front” ta yi tir a harin na ‘yan sahayoniya wanda ya yi sanadin shahadar Birgediya janar Khalaf Jasim, tare da cewa; ci gaba da wuce gona da irin na ‘yan sahayoniya akan kasar Syria.
Kungiyar ta nuna cikakken goyon bayanta ga Syria tare da yin kira ga dukkanin al’ummar larabawa da su yunkura domin taimakawa Syria a fadan da take yi da ‘yan sahayoniya.
Tags:
Labaran Duniya