@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA GARIN NEMAN GIRA A RASA IDO
Allah ya kawo mu cikin watan Ramadan wanda zuwa gobe asabar 25-4-2020 ba za a sami wani da ya rage ba tare da azumi a bakinsa ba. Dalili kuwa shine, mutane da yawa basu ga watan Ramadan da idanuwansu ba jiya alamis, saboda haka basu yarda da sanarwar Sarkin Sokoto ba, kamar dai yadda masu yarda da sanarwar sarki Sokoto suka qaryata masu ganin wata ranar laraba.
Da iznin Allah yau kowa zai ganshi a zahiri, saboda haka gobe kowa zai tashi da azumi.
Rudani na biyu kuma da za a soma fuskantarsa tun daga yau shine, batun shan ruwa (buda baki ko Ifdar), domin alqawarin shaidan ne sai ya halakar da dukkan wadanda suka bi shi ta hanyar biyewa son zuciyarsu.
Sunqi daukar azumi a ranar farko, yanzu kuma zai cigaba da qawata musu karya azuminsu da sunan dabbaqa sunnah.
Allah (T)dai yayi umarni cewa mu cika azumi zuwa dare,
(Baqara, aya ta 187)
LATSA NAN👇
☞ ͡Saɓanin Ganin Watan Ramadhan ko Shawwal
☞ ͡Hukuncin wanda yaƙi ɗaukar Azumi, Alhali yana da labarin ganin Wata
☞ ͡Gaskiya da Gaskiya Mun raba kayan abinci Tiraila 276, a jahohi Uku – Minista Sadiya
Shi kuma Shaidan ya qawata musu cewa su sha ruwa kafin dare don su saba umarnin Mahaliccinsu, kuma sun amsa masa wannan kira nasa da yayi musu da babbar murya.
Kada ku yiwa Annabi (S.A.W.W)qaryar cewa wai shi yayi muku wannan umarni na sabawa Mahalicci, domin Umar Bn Khaddab da Usman Bn Affan sun qaryata wannan tatsuniyar a aikace.
Domin su ba sa shan ruwa har sai bayan sunyi sallar magrib, sabanin yadda ku kuke sha kafin sallar magrib.
(MUWADDA MALIK, babin gaggauta buda baki da jinkirta sahur).
Ko da shike ban san wandanda suka fi yin koyi da Annabi (S.A.W.W)ba tsakanin su da ku.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~24th April, 2020.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa