@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AN TSARE SAYYID ZAKZAKY (H)KUNA MARNA
Son kai da bin son zuciya da rashin damuwa da halin da wani ya fada ciki saboda zaluncin shugabanni ya zama dabi'a irin ta dan Adam.
Hakan kuwa ya saba koyarwar addinin muslimci wanda fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W)yazo mana da shi.
Ya kasance (S.A.W.W)na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ DUK WANDA BAI DAMU DA HALIN DA MUSULMI KE CIKI (na qunci )BA, BA YA DAGA CIKINSU .‘’
KARANTA WANNAN:
Yahudu sun cimma manufar su 80% da wannan cutar ta Coronavirus
Hikima kayan mumin Part 2
To, ina kuma ga halin da muminai ke ciki?
Babu mai musu cewa Sayyid (H)na cikin mummunan yanayi na quncin rayuwa sakamakon zaluncin azzaluman mahukunta wannan qasa Nigeria, amma maimakon a tausaya masa sai ji kake daga bakunan wasu na cewa , ‘’ ALLAH YA QARA !‘’
Ga dukkan mai yin da'awar gaskiya irin wacce Annabi (S.A.W.W)yazo da ita, to, ya san cewa akwai irin wannan jarrabawa da take samunsu kamar yadda ta sami Manzanni (A.S)gabaninsu.
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ SUNNAR ALLAH CE WACCE TA GABATA, BA ZA KA TABA SAMUN CANJI CIKIN SUNNAR ALLAH BA, KUMA BA ZA KA TABA SAMUN MUSANYE CIKIN SUNNAR ALLAH .‘’
Saboda haka duk da irin wannan qunci da Sayyid (H)ke ciki, to, tare da shi akwai aminci cikin zuciyarsa cewa akan gaskiya yake.
Yanzu ga shi ku ma Allah ya kawo muku wani salo na takurawa daga azzalumar hukumar da kuke yim murna da ayyukanta, musamman ma ku mazauna ABUJA da KADUNA.
Ba murna muke yi ba, domin wannan bala'i ya shafi wadanda ma aka dade ana zaluntarsu, da kuma wadanda ba sa goyon bayan zalunci.
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ KU JI TSORON FITINA WACCE BA WADANDA SUKA YI ZALUNCI DAGA CIKINKU KADAI TAKE SHAFA BA.‘’
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~3rd April, 2020.