Ku tambaye ni kafin ku rasani Fita Na (2)






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MENENE ABINDA YAFI SAMA GIRMA ?

Cikin tambayoyin da Yahudawa suka yiwa Imam Ali (A.S)don su qure shi game da cewarsa, ‘ SALUUNIY QABLA AN TAFQIDUUNIY ‘’

Ga tambayoyin da suka yi masa kamar haka;

‘’ Wanne abu ne ya fi sama girma?

Kuma wanne abu ne ya fi qasa fadi?

Wanne abu ne mafi rauni (weak)fiye da maraya ?

Wanne abu ne ya fi wuta zafi?

Kuma wanne abu ne ya fi qanqara sanyi?

Wanne abu ne ya fi kogi wadata?

Sannan kuma wanne abu ne ya fi tsauri (tauri)fiye da dutse ?‘’

Sai Imam Ali (A.S)ya basu amsa kamar haka;

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Tuhuma akan kubutacce , shi yafi girma fiye da sama (duk mutumin da ba shi da laifi sannan kace za ka tuhume shi, to, ka tunkari aiki mafi girma. Sayyid Zakzaky (H)babban abin misali ne).

Kuma gaskiya ita tafi qasa fadi (domin duk tafiyarka ko gudunka ba ka isa ganin qarshenta ba).

Mai annamimanci na qarya shine mafi rauni fiye da maraya, (domin duk lokacin da asirinsa ya tonu sai ya fi maraya zama abin tausayi).

Kuma kwadayi ya fi zafi fiye da wuta, (tambayi kwadayayyu kaji abinda suke ji na zafi cikin zuciyarsu idan sun rasa abinda suka so a basu).

Kuma buqatarka zuwa ga marowaci ita ta fi sanyi fiye da qanqara, (domin ba baka zaiyi ba, kuma kai za ka qasqantar da kanka ta kowacce fuska don ka sami abin hannunsa).

Gangar jiki mai wadatar zuci , ita ta fi wadata fiye da kogi (domin kogi komai cikarsa bai qi ya samu qari ba, shi kuma mai wadatar zuci yana iya haquri da gamsuwa da qanqanin abinda ta samu).

Sannan kuma zuciyar kafiri tafi tsauri fiye da dutse, (zuciyar Fir'auna da ta Buhari kyakkyawan abin misali ne).‘’

(MUNTAKAB SIRATU AHLIL BAIT, SH:121-122)

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~20th April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post