@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ABUBUWA UKU DA MAHAIFA BA TA 'DAUKE SU BA
Wasu don neman sani, wasu kuma so suke su qure Imam Ali (A.S)don yace duk tambayar da akayi masa zai bada amsarta ta yankan shakku.
Wata rana wani mutum da ake kiransa KA'ABUL AHBAR ya tambayi Imam Ali (A.S)cewa;
(1)- Ya bashi labarin abinda ba shi da Uba a gare shi.
(2)- Da abinda ba shi da dangi.
(3)- Da abinda ba shi da alqibla.
Sai Imam Ali (A.S)yace da shi;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah
‘’(1)- Abinda ba Uba gare shi shine Annabi Isah(A.S).
(2)- Wanda ba shi da dangi kuma shine Adam (A.S).
(3)- Abinda babu alqibla gare shi kuma shine dakin Ka'aba .‘’
Ka'aba ce alqibla, don haka babu alqibla gare ta.
Daga nan sai wannan mutumi ya qara tambayarsa cewa;
Ya ba shi labari kan abubuwa uku da mahaifa ba ta dauke su ba.
Sai Imam (A.S)yace masa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ (1)- Sandar Annabi Musa (A.S)(wacce ta zama macijiya ba tare da haihuwarta aka yi ba).
(2)- Taguwar Annabi Salihu (A.S)(wacce Allah ya kirata da NAAQATU SALIHU).
(3)- Da Ragon Annabi Ibrahim (A.S)(wanda Allah ya fanshi Annabi Isma'il da shi).‘’
Sai ya qara yi masa tambayar qarshe yake ce masa; ‘’ Akwai wata tambaya wacce matuqar ka amsa min ita zan sallama. Abinda nake so shine, ka bani labarin Qabarin da yayi tafiya da mai shi .‘’
Sai Imam (A.S)yace masa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ WANNAN SHINE YUNUS IBN MATTA, WANDA ALLAH YA TSARE SHI A CIKIN KIFI.‘’
(Kunga anan Kifin ya zama shine qabari, domin yana dauke da Yunus (A.S), kuma Annabi Yunus shine me qabarin).
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~21st April, 2020.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi