Ku tambaye ni kafin ku rasa ni – Imam Ali (AS)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MENENE ALAMAR MUMINI ?

Daga cikin gargadin da Imam Ali (A.S)ke yiwa jama'arsa shine, su bambaye shi kafin su rasa shi, domin idan suka rasa shi sun rasa alkhairori da ilimi masu yawa.

Saboda hakane ma wata rana yayi wannan gargadi a masallaci sai ga wani mutum ya keto cikin jama'a ya tambaye shi a masallaci cewa;

‘’ Yaa shugaban muminai, ka nusar dani a bisa wani aiki da idan na aikata shi zai kubutar dani daga wuta .‘’

Sai Imam Ali(A.S)yace masa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Yaa kai wannan mai tambaya, ka saurara ka ji sannan ka fahinta, kuma ka sami yaqini.

Ita duniya ta tsayu akan abu uku ne;

(1)- Mai ilimi da yake magana yake aiki da iliminsa.

(2)- Da mawadacin da ba ya rowa ga ma'abota addini.

(3)- Da faqiri mai haquri.

Idan mai ilimi ya rufe iliminsa, mawadaci ya hana dukiyarsa, kuma faqiri bai yi haquri ba, to, duniya a wajenta akwai azaba da tabewa.

Yaa kai mai tambaya, kada rudu da yawan masallatai da jam'in mutane, jikkunansu suna hade, amma zukatansu a rarrabe ya rude ka, domin mutane kaso uku ne; mai gudun duniya, da mai kwadayi da kuma mai haquri.

(1)- MAI GUDUN DUNIYA:- Shi mai gudun duniya ba ya murna da wani abu na duniya, kuma ba ya baqin ciki da wani abu na duniya da ya kubuce masa.

(2)- MAI HAQURI:- Shi kuma mai haquri yana burinta (duniyar)idan ya sami wani abu daga gare ta sai ya kautar da kansa a bisa ita, saboda ya san mummunan qarshenta.

(3)- MAI KWADAYI:- Shi mai kwadayi kuwa, ba ya damuwa da dukkan abinda ya samu, halas ne ko haram (duk daya ne a gurinsa). ‘’

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Sai mutumin ya qara ce masa, menene alamar mumini ?

Sai Imam (A.S)yace masa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ (Shi mumini)YANA BINCIKE AKAN ABINDA ALLAH YA WAJABTA MASA NA GASKIYA, SAI YA AIKATA SHI. KUMA YANA BINCIKE AKAN ABINDA YA SABA MASA, SAI YA KUBUTA DA SHI .‘’

Sai mutumin yace, ‘’ Wallahi ka yi gaskiya yaa shugaban muminai .‘’

Sai mutumin ya bace, aka neme shi ba a ganshi ba.

Sai Imam (A.S)yayi murmushi yana kan Mimbarinsa, sannan yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ WANNAN 'DAN'UWANANE KHIDIR (A.S)(wanda yayi zamani da Annabi Musa (A.S)).‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

~19th April, 2020.  KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post