Ko kun san wa ake kira mai Hankali???






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AUNA KANKA KA GANI KO SHINE

Ba wai don kaga mutum na tattara ledoji akan bola ne za ka kira shi mahaukaci ba, da za ka tambaye shi dalilin tattara wadannan ledoji kafin yanke masa hukunci zai fi zama adalci.

Yanzu an shiga wani zamani wanda talauci kan sa mutum ya riqa yin aiki irin na mahaukata alhali kuwa ba ya daga cikinsu.

Wani kuma za ka ganshi kamar mai hankali amma mahaukaci ne wajen Allah, wanda ya zama mahaukaci wajen Allah kuwa shine babban mahaukaci.

Allah (T)ya siffanta mana masu hankali cikin Alqur'ani, saboda haka in kai ba haka kake ba to, ka zama cikakken mahaukaci.

KARANTA NAN: 
Masoya Buhari, tamkar masoya Fir'auna ne a zamanin sa!
Nazari akan Rayuwar Aure Part 1
Ko kun san wa ake kira mai hankali??

KARANTA KA GANI 'DAN'UWA

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ LALLE WADANDA SUKA NISANCI 'DAGUTU GA BAUTA MUSU(ta hanyar qin yi musu biyayya kan zaluncinsu), KUMA SUKA MAIDA AL'AMARI GA ALLAH (komai cutarwar da ake yi musu), SUNA DA BUSHARA. TO, KA BAYAR DA BUSHARAR (Aljannah)GA BAYINA.

WADANDA KE SAURARON MAGANA (ta hanyar wa'azi da ake yi musu), SA'AN NAN SU BI MAFI KYAWUNTA. WADANCAN (masu sauraron)SU NE ALLAH YA SHIRYAR DA SU, KUMA WADANCAN SU NE MASU HANKALI .‘’

(Suratul-Zumar, aya ta 17-18)

Amma yanzu kana samun wasu wadanda in kaga suna sauraron wa'azi, to, na dan qungiyarsu ne, su kuma suna son kowa ya saurari nasu wa'azin.

Saboda haka duk wanda ya saurari wa'azinsu sannan yabi abu mai kyau daga abinda suka fada, kuma ya watsar musu shiririta na daga maganganunsu, to, shine shiryayye kuma mai hankali.

Amma su masu qin saurare daga wasu ballantana su sami maganar dauka daga cikinta, sune wadanda Allah ya batar, kuma sune mahaukata!

Domin sai ka saurari magana kake fahintar abinda mai maganar ke cewa na shiriya.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~7th April, 2020.


IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post