Kira gare mu mata, mabiya Malam Zakzaky dake amfani da kafar sada zumunta





Yaseerah baseeru shi'eet 🖊

Duba da yadda addini yake da bukatuwa garemu ne yasa nazaɓi nayi wannan rubutun, don ƙwadaitar da ƴan uwana sister

Allah (t) cikin ikon da da buyayewar yayi mana wata baiwa mai girma, baiwar kasancewar mu mata da Kasan cewar duniya tana tafin hannun mu, se inda mukaso mu juya ta.

Haƙiƙa mace tana da abinda zata bada gudummawa a addini, fiye da gudun mawar da duk wani namiji zai bada.

Sannan dayawan abubuwa muna ƙinyi ne bawai dan bazamu iya ba, sedan kawai munji bazamu iya Ba.

Natuna wasu maganganu na imam Khumaini dayace .

أن للمرأة دوراً كبيرا في المجتمع والمرأة مظهرة لتحقق آمال البشر .

Sannan Imam ƴakara dacewa,

من أحضان المرأة ينطلق الرجل نحو السمو.


 A zamanin nan mace ko hello taje ta rubuta a posting nata sai kaga tasamu comments da like dayawa, wanda hakan ke nuna mutane suna karanta abinda tayi.

To meyasa bazamuyi anfani da wannan damar da falala da Allah yayi mana ba, wajen yada mazlumiyar Sayyid

Nasan babu wata ƴar uwa ta mace dazata rasa abin rubuta wa koda layi 2 ne dangane da abinda akaiwa sayyid.

To meyasa bazamu dinga rubuta wa ba? Menene amfanin mushare awowi muna magana da wadanda ko sanin su bamuyi bama' ?

Mai makon ɓata lokacin chat da muke, to muyi anfani da damar man wajen yin aikin Addini.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Naji Sayyid yace kayi iya abinda zaka iya wajen dafawa addini, koda shayi zaka iya rabawa to shin ƴar uwa ta idan kin tambayi kanki mai kike yi wanda addini yake cigaba ta silar ki!!!


Kudi muke sawa musai data, to meyasa Bazamu ci moriyar kuɗin mu ba, ta hanyar yin aikin Addini?

Koda bakiyi karatu va' to zaki iya yin abinda zaki yaɗa zaluncin da akai wa Sayyid, ta hanyar yin shearing na rubutan wasu.

Mene zai rage ki dan kinyi copy na rubutun wani wanda yayi akan sayyid kinyi posting?

Muyi ƙoƙarin samawa kanmu amsa idan Mala'iku suka tambaye mu a kabari, shin da kika sai waya mai dame dame kikayi?

إِنَّمَا أَمْرُهُمْ إِلَى اللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُوا يَفْعَلُونَ

Kowa zai bada labarin abinda yakasance yana aikatawa.

Kenan idan aka zo aka tambayan saina ce na share Shekaru inna ta chat da wasu wanda ko sanin su ma banva ?

Bawai nace magana da wasu baida muhimmanci ba, sedai musamu wani abunda zamu riƙe lokacin daza a ce.

وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَ

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post