Jiragen Saudiyya Sun Kai Hari Sau 300 A Yemen

Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa a cikin kwanaki bakawai da suka gabata, sojojin Saudiyya sun kai hare-hare kimanin 300 kan yankuna a kasar Yemen.

(ROHOTON ABNA24.com) Kakkain sojan kasar ta Yemen birgediya Janar Yahya Sari’i  ya fadawa tashar talabjin ta al-masiriyya cewa sojojin kawancen Saudiyya sun kai hare-haren ne a lardunan San’aa, Bayda da kuma Ma’arib, inda suka kashe fararen hula da dama.

Yahyah Sari’i ya kammala da cewa sojojin kasar suna shirin maida martani nan ba da dadewa ba. Ya kuma kara da cewa dole ne mu kare mutanemmu mu kuma kare kasarmu daga makiya.

Tun cikin watan Maris na shekara dubu biyu da sha biyar ne gwamnatin kasar Saudiyya tare da takwarorinta na kasashen Larabawa kimanin goma suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abbdu Rabbu Hadi Mansur kan kujerar sugabancin kasar.

Yakin dai ya yi sanadiyar jefa mutane kimani miliyan ashirin da hudu cikin yunwa a kasar inji rahoton majalisar dinkin duniya, Sannan wasu miliyoyi kuma suka zama yan gudun hijira.

KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post