DA SUNAN ALLAH MAI MURQUSHE AZZALUMAI!
Ya ’yan uwa Musulmi maza da mata! Assalamu alaikum warahmatullah.
An ruwaito cewa Sayyidina Ali dan Abu Talib (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Ya ku mutane, haqiqa Manzon Allah (S) ya ce; “Idan wani ya ga wata hukuma (gwamnati) ta maida zalunci aikinta, ta keta haddodin Allah, ta shuka kiyayya ga sunnar Manzon Allah, tana aikata barna da zalunci a tsakanin bayin Allah, to a wannan hali duk wani wanda bai yi amfani da hannunsa da bakinsa ya yi yaki da wannan zalunci da barna ba, to ya sani, Allah zai kai shi matsugunin wannan Jagoran gwamnatin, ya sa duk cikar su a wuta!”.
To, ga shi gwamnatin kasar nan ba ma kawai ta maida zalunci aikinta ba ne, a kan zalunci ne ma aka gina ta, ba ma kawai ta keta haddin shari’ar Allah ba ne, ta aje shari’a ne waje guda ta dauki shari’ar da mutum ya tsara, ba ma kawai ta karya alkawarin Allah ba ne, tun farko ma ba ta dauki alkawari din ba! Ta ki ta dau alkawarin Allah, ta yi wa Allah tawaye, amma ta dauki alkawarin Dagutu. Ba ma kawai tana aikata barna da zalunci a tsakanin mu ba ne, a a, ta ma mai da wannan zalunci adalci ne!
KARANTA NAN:
◉Masoya Buhari, Tamkar masoyan Fir'auna ne a zamanin sa!
◉Nazari akan Rayuwar Aure Part 1
Ba shakka mu kuma ba ma kawai mun ki yin amfani da hannuwanmu da bakunanmu don mu yaki wannan zalunci da barna ba ne, mu ne da kanmu muka yarda ta aikata wannan barna da zalunci a kanmu! Mu ne fa muka zabi wannan azzalumar gwamnati da hannuwanmu, kuma muke goyon bayanta da bakunanmu. Kun ga ashe mune muka ba shugabannin gwamnatin damar su zalunce mu, su kau da shari’ar Allah waje guda, su dauki shari’ar da mutum ya tsara. Mune muka ba su damar su aikata barna da zalunci a tsakaninmu, kuma su mai da wannan barna da zaluncin halal! Ba ma kawai mun ki yin amfani da jikinmu da bakinmu don mu yaki wannan hali ba ne, a maimakon haka, mu ke karfafa musu gwiwa su ci gaba!
To, ’yan uwa Musulmi! Idan wannan hadisi ya ce duk wanda ya ga wani shugaba yana zalunci, amma ya qi ya yaqe shi da ayyukansa da bakinsa, to ya sani fa makomarsa daya da wannan azzalumin Shugaban, to ina ga mu? Kun ga ashe ba ma kawai yana ga Allah ya dauke mu Ya kai mu mazaunin wadannan azzalumai, Ya sa dukkanmu a wuta ba ne, ai mu da kanmu ne ma azzaluman!
E mana! Don me ba zan ce haka ba? Mune fa muka zabi wannan gwamnati, kuma muna jin cewa tamu ce. Mun sa mata suna “Gwamnatin mutane, wadda mutane suka yi, domin mutane.” Kuma muna jin mune mutanen, da mu da gwamnatin duk abu daya ne!
A wannan hali ta yaya za mu iya cewa shugabannin ne kurum azzalumai, amma mu ba ruwanmu? Da mu da shugabannin (wato ina nufin) shugabannin kananan Hukumomi, da Gwamnoni da Shugaban kasa duk cikar mu azzalumai ne, kuma duk cikar mu masu laifi ne!
Don me hakan ba zai zamo kashin gaskiyar al’amari ba, alhali Allah Madaukaki ya tsara, kuma ya kammala, kuma ya saukar mana Alkur’ani mai girma, amma mu muka ki kememe, muka zaba wa kanmu tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya? Tsarin mulki wanda mutum Hamsin ba Daya (49) suka tsara mana, kuma wakilanmu wadanda muka zava suka je suka zartar mana! Alhali Allah Ya shirya mana Musulunci ya zama hanyar rayuwarmu, amma mu muka ce a a, mu dimokradiyya muke so. Alhali Allah Madaukaki ya zartar da dokar cewa shari’arSa za mu yi amfani da ita (a tafarkin rayuwarmu), amma muka watsar, muna aiki da dokoki na Turawan Ingilishi! Ga shi Allah Madaukaki Ya hore mu da mu nemi gidan lahira, amma muna jin mun gamsu da rayuwar wannan duniya kamar nan ne matabbata!
Bilhasali ma, me zai sa hakan ba zai zama kashin gaskiya ba, alhali Allah Madaukaki Ya hukunta cewa shi ne kawai za a bautawa, amma mu a maimakon haka kasa muke bautawa!
Ya ’yan uwa Musulmi! Mai yiwuwa ne abin da nake fadi ya yi maku wuyar ganewa, amma wallahi gaskiya nake fadi! Mai yiwuwa ku ga kun kasa yarda, amma a gaskiya a halin yanzu muna zaune a cikin kafirci ne. Musulunci kam babu shi a wannan kasa! Musulunci a wannan wuri sifili (zero) ne, a gaskiya ma bai kai sifili ba a nan. E mana!
Muna dai da guggubin Musulunci, wanda ke cakude da al’adun kakanninmu da kuma tsarin Jahiliyya, wanda Turawan mukin- mallaka suka kawo. Guggubin kuwa ko an tara ba zai zama daidai da komai ba. Misalin Musulunci a wannan kasa kamar jirgin sama ne da ya fado ya kone kurmus. Guggubinsa da suka ragu ba za su yi daidai da jirgi guda ba. Ko kuma ana iya tara guggubin waje guda jirgin ya tashi? To haka, Musulunci yake a wannan kasa.
Ba zan zauna ba sai na yi maku bushara cewa, akwai wani hadisin Manzon Allah (S) inda yake cewa: “A farkon kowane karni, Allah zai tada wani da zai jaddada wa wannan al’umma addininta.” To Alhamdulillahi kwanan nan muka shiga sabon karni, wato karni na 15. Saboda haka ne ma muka zabi taken wannan taro ya zama a kan karni na 15 ne, kuma wannan taro shi ne irin sa na 25 da wannan kungiya (ta MSS) ta yi. A cikinsu biyu ne kawai aka yi a wannan sabon karni. Taken wancan taro na baya shi ne Imani, wato makamin da muke bukata don rusa wannan kafirci. Kuma fatanmu shi ne mu ga bayyanar wannan Mujaddadi, wanda Manzon Allah (S) ya gaya mana cewa Allah ya yi alkawarin (tayarwa a bayan kowane karni).
Wassalamu alaikum wa Rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuh.
Auwal Yusuf Muhammad
Ma'asumah Najeria news Updet
#6/4/2020
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky