Abbagano✍
mutuƙar kaji kana murna da kisan ƴan shi'a to gaskiya kabin ciki kanka, anya kai Musulmi ne? Anya akwai ƙwaƙwalwa akan ka kuwa? Anya kana da adalci?
Idan kai Musulmi ne to meyasa zakai murna da kisa alhali musulunci yahana ayi kisa, kisan kuma ko wanne irin rai, ne.
Ko baka karanta ƙur'ani ne?
( وَلَا تَقْتُلُوا النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ ۗ وَمَن قُتِلَ مَظْلُومًا فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِ سُلْطَانًا فَلَا يُسْرِف فِّي الْقَتْلِ ۖ إِنَّهُ كَانَ مَنصُورًا )
(Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.)
Kaida addinin ka yahana kashe rai kowanne iri ne, to ina kai ina murna da kashe ɗan uwan ka musulmi?
LATSA NAN👇 ☞ ͡Ku cika azumin ku, zuwa dare" – Faɗar Allah (T)
☞ ͡Iyali A Muslunci... Fita Na Uku (3)
☞ ͡Hukuncin Shan Ruwa
Idan anyi magana sai kuce suna zagin Sahabbai!!! To shin a ina akace sharaɗin zagin Sahabbai kisa ne? Idan ma ya tabbata suna zagin!!!
Da'ace hukuncin zagin sahabi kisa ne da tun zamanin Annabi Muhammad za'afara kashe kashe, domin tun sannan akafara.
Azzalumai sunyi zalunci sai kuma kuzo ku goyi bayan su, to kunjawo kanku ne, tun a duniya dama gobe lahira.
Idan sun gama kisan ƴan shi'a din ai kanku zasu dawo, tunda su basu iya komi ba sai kisa, kuma babu wanda waɗanda suka saba kashe wa, sai su juyo kanku.
A ranar ƙiyama kuma Allah daman Yagaya muku idan kuka goyi bayan azzalumai to kuma zata shafe ku.
( وَلَا تَرْكَنُوا إِلَى الَّذِينَ ظَلَمُوا فَتَمَسَّكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللَّهِ مِنْ أَوْلِيَاءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ )
Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN