Iyali A Musulunci.. Fita Na Uku (3) Zama A Gidan Iyayen Miji ko Mata Bayan Aure



Daga: Bin Haroun Sigau

Al'ummar Musulmi, kamin kamun Jari hujjah, sukan yiwa ɗiyar mace ko namiji aure, kana su zauna a gidan iyayen mijin ko kuma shi miji ya zo su zauna tare a gidan iyayen matar tasa, a matsayin su na sabbin aure.

Ta yadda zasu gamsu, da kuma kasance wa kusa da manyan mutane. Wanda zasu ke saka su kan hanya, da koya musu abubuwan da suka shafi zamantakewar aure ba tare da damuwar wannan gida mallakin iyayen mace bane ko abinda yayi kama da haka.

Amaren zasu zauna a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, kuma dukkan su zasu ke taimakawa ta wajen tafiyar da Ayyukan gida. Sabida wannan aure mai sauƙi ne, musamman ta ɓangaren gyare-gyare, sabbin amare zasu koyi duk wasu abubuwan buƙata daga halayyar manyan su a cikin gida.

Wasu kuma zasu zauna a sabon gida, wanda shi wuri kyauta ne, musamman sabon guri. A zamanin kawai zuwa zakai ka sari iya ƙarfin ka. Kamar yadda yazo cikin faɗin Allah madaukakin sarki, "ƙasa ta Allah ce, da duk wanda yake zauna akan ta."
Tsarin gine-ginen su masu sauƙi, ba kuma irin ginin tunƙaho bane, bugu da ƙàri babu tara daga gwamnati, ko neman izini ko wani abu makaman cin haka.

Wanda in muka kwatanta da wannan zamani namu, abubuwa sun sha bambam da wancem zamanin. Wanda yanzu komi tsada ne, bayan kasai fegin gini, kana ginin ma za'a zo ace; Kasupda tace kaza, saika gyara ko ka bada kudi a barka kaci gaba da ginin.

Na taba ji, a wancen zamanin wasu mutane dake zaune a Karbala da basu wuce mutum dubu ɗari ba. Duk tarin su bazaka sami mazaje da suka kai huɗu wanda basu da aure ba. Amma a wannan zamani akasin haka ne, mun biye wa son rai da rashin haɗin kai ga yawan matasa ba aure, ba kuma babu yadda za'a yi bane iyaye n sun saka burace-burace kan ƴayan su.

 READ THIS👇
☞ ͡Hukuncin wanda yaƙi daukar azumi, alhali yana da labarin ganin wata
☞ ͡Yawan mutane, bashi ne ma'aunin gane gaskiya ba
☞ ͡"Kuma ku cika azumi zuwa dare" – Faɗar Allah (T)

Zinace-zinace ya zama kayan ado, wannan yasa yanzun komi ya rincaɓe, rayuwa ba daɗi, komi yayi tsada, ga kuma al'umma kullum cikin barazanar kisa da ɗauri ba ba gaira ba dalili, ba tare kuma da kayi laifin komi ba. Tabbas, dolen mu in muna son rayuwa tayi kyau, mu zama cikin aminci a tsakanin mu, mu tashi tsaye ya zama addini ne ke iko damu. Addinin ya zama shike sarrafa mu da kwakwalen mu. Ta yadda, da an kalli ayyukan mutum, za'a ga Alqur'ani a aikace.

Yanzu bama ka zauna a gidan iyayen amarya ba, gidan ku na gado ma ba kasafai zai zaunu maka ba. Sabida hange-hange, gutsiri tsoma, da hassada. Kaga ɗan uwan ka ne ke gaba dakai, ko kuma yake baƙin ciki da yaga kana samun ci gaba a rayuwa.
Baya ga haka, tarbiyyar yaran ka tabarbare wa zata yi, kana basu tarbiyya, ana lalata maka ginin da kake.
Ina koyarwar Manzon Allah (S)?? Tuni mun watsar, muna nema mu koma zamanin jahiliyyah.

Gara zamanin jahiliyyah ma wallahi, domin su lokacin ɗan aike bai zo musu ba, amma abin takaici mu ga Qurani a tare damu, har muna tutiya da muna bin sunnar Manzon Allah da ƙoƙarin koyi da ɗabi'un sa. Sai kuma ya zama a baki ne kawai, amma a aikace aikin da maƙiya addinin nan suke tun cen baya muke ci gaba dayi, na ganin mun ɓata sunan addinin, da maida shi addinin a wata irin kama.

Aure ibada ne kuma Sunna mai karfi na Manzon Allah (S), da yawa mutane kan ɗauki aure a matsayin hanyar samun sauƙi da jin dadi ne. Mukan manta da Faɗin Allah (T) da yake cewa; "Ban halicci aljani da mutum ba, sai son su bauta min." Da zai zama komi na rayuwar ku kallon sa a matsayin hanyar bauta wa Allah muje da kun tsira. Amma Sam bamu ɗaukar sa matsayin ibada, wannan shike kawo tabarbarewar mafi akasarin zaman aure. Da muna ɗaukar sa ibada, da komi za muyi sai mun nemi ilimin sa, da kuma yin ƙoƙarin kiyaye dokokin Allah a ciki.

Hankalin da Allah yayi mana babbar hujja ce akan mu, ko da Allah bai aiko mana Manzo ba, hankalin da yayi mana ya isa ya zama hujjar dazai ƙona mu da shi. Dalili kuwa shine; hankali yakan fayyace maka ƙarya da gaskia, saidai kawai kaƙi binta don raɗin kanka, ko wani mai tunjumenen rawani ne ya kalle ka ya jawo maka hadisan ƙarya, kana saka hankali zaka iya yin hukunci cikin maganar sa, ka gane gaskia ne ko ƙarya yake.

Ba yin aure ne ba kawai, a'ah kaji kai auren nan

da kayi ko zakayi ibada ne kuma zaka yi iya ƙarfinka don sauke nauyin daya rataya a wuyanka, haka ka matan. Domin yanzun mafi akasarin matasan mu, sukan yi aure ne don kawai biyan buƙatar su da sha'awa, da zarar mace ta tsufa saika gan an fara wukaƙanta ta, ana shirin bata jan kati, don a shigo da sabuwa. Ba tare da damuwa da gane cewa; ibada zasu yi ba, wannan yayi tasiri gaya a kwakwalen mutane...

Allah shi kyauta, ya kuma bamu ikon yin biyayya kan dukkan abinda ya umurce me. Ya Allah muna roƙon ka ga gaggauta kwato mana jagoran mu Sayyid Zakzaky (H) a hannun Azzalumai, ka bashi lafiya da nisan kwana. Ka saka masu son ganin bayan shi yaga bayan su, Allah waɗannan azzalaumai ka saka suyi mummunan ƙàrshe. Wa sallàllahu ala Muhammad wa alihiɗ ɗaahiree..l

Ci gaba.....

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post