Sauƙaƙa Sadaki...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Daga: Bin Haroun Sigau
Yazo a ruwaya Manzon Allah (S) yace; "Mafi Girma a cikin matan al'umma ta, itace wacce take da hasken fiska, da kuma ƙarancin sadaki."
Wannan a hankalce ma, ba tare da kawo Hadisi ba ga matashi da matashiya da suke da buƙatar gina iyali, sadaki ba wani abu ne ba illa ɗan abinda kawai da za'a ayyana domin bada muhimman ci wa wannan aure, ko yaya ko abinda aka ayyana ɗin yake. Babu wani abu da zai iya kange zukata biyu, sa'ilin da suka faɗawa soyayyar junan su, koda kuwa ƙarfin su ba daya ba, domin ita zuciya da so ba su ginu kan matsayi ko mulki ba, sun ginu ne kan muradi da kyakkyawar fata.
Idan mukai duba ga sauran mutane yanzun sun maida mata kamar dabbobin kiyo, zaka ji ana kiram ma yarinya manyan kuɗaɗe da ba sune zasu riƙe igiyar auren ba. Hasali ma, a wannan nahiya tamu ta hausa, in mace ta kasance lokacin auren ta miji ya biya sadaki mai kauri, zai wuya kaga rayuwar auren ta ginu ne akan sona haƙika. Yawanci ana amfani da kuɗi ne don saye zuciyar yarinya da iyayen ta, wanda hakan zai iya kawo naƙasu ga iyalin da ake so a gina su kan addini, don auren zai zama kan soyayyar kuɗi ne, ba soyayya don Allah ba. Shi kuma aure ibada ne, din haka ake son gina shi a bisa hanya mafi kyau (Muslunci) don damar da iyali ababen alfahari.
Muslunci addini ne da yazo da sauƙin sauƙaƙawa, ta yadda kowa zaiyi rayuwa daidai ƙarfin sa, kuma har ya zama ma yana tarayya da wanda suka fishi ƙarfi a wajen ibada da sauke haƙƙin Allah. Matan zamanin nan suna son auren mai kudi, sai bayan anyi aure su fahimci neman kuɗin sa yafi masa zama da matar sa yayi fira. Wanda in abin ka sami talaka ne bawan Allah mai wadatacciyar zuciya zaka samu, rashi ko samu bazai taɓa tauye masa bawa iyakin sa lokaci ba. Domin yasan abinda kawo su gidan silar sa ne, kuma da farin cikin sa zasui farin ciki.
A muslunce kana iya bada zobe a matsayin sadaki, ko uban yarinya ya baka wani kayi, yace ladan aikin shine zai zama sadakin auren ka da ɗiyar sa, ko wani abu makamancin haka, abinda bazai yiwu ba shine a ɗaura maka aure da wata ba tare da an ayyana wani abu matsayin sadakin ba.
DUBA NAN:
☞ ͡Iyali A Muslunci... Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa Ni Part (3)
☞ ͡Wannan Harkar tana koyar damu riƙon amana ne!
Kamar yadda wasun mu suka jahilci lamarin sadaki, zaka ji ana cewa; uba yayi sadaka da ɗiyar sa. Kunsan me haka yake nufi?? Ya aurar da ita babu sadaki, me zamu kira wannan aure??? Ana aure ba sadaki ne?? Wajibi ne ya zama an biya sadaki, in kuma shi uba, yace; zaiyi sadaka ne, sai yayi wani abu guda ya ɗauki sadakin ya baiwa wanda zai auri ɗiyar tasa, in aka zo wajen aure, shi ko wakilan sa su bawa uban yariya ɗin matsayin sadakin da ya kamata a bada, shikenen. Don yawancin matasan mu suna son aure amma tsaurara sadakin da ake shike sare musu guiwa.
Sauƙaka sadaki, yakan haifar da farin ciki, cikin iyali ba tare da taƙura wa ba, in akai aure saika ga, miji da mata suna farin ciki ta haka ma, kowa ƙoƙari yake wajen ya nemo abinda zasu rufa wa juna asiri. 'Allah yana so muku saukí, kuma baya son wahala.' Magana makamancin wannan yazo daga Manzon Allah (S) yace; "Ku maida abubuwa masu sauƙi a tsakankanin ku, kada ku maida su masu wahala."
Sauƙi a komi yakan kawo ci gaba da karancin gajiya wa, a zahiran ne ko a hankalce. Dangane da maganar Hasken fiska da Manzon Allah (S) yayi a ruwayar dana kawo a farko, yana nufin kyawawan ɗabi'u, wanda shine ke haskaka fuskar mutum da kuma fatar sa. Wannan ba sabon abu bane tsakanin Musulmi tun kafin shigowar shugaban cin jabbiran mahukunta bayan Manzon Allah, zaka samu sadaki wani ɗan abu ne ake badawa kaɗan kuma mai sauƙi, saidai in da wani dalili.
A zamanin khalifancin Ummayyawa da Abbasid sun sauya abubawa na daga koyarwar Muslunci da yawa zuwa ra'ayoyin Sarakuna kamar Sarkin Persia musamman ta ɓangaren sadaki. Sabila da haka Imam (As) yake ƙara ƙarfafa mutane kan Sadaki bisa yin irin yadda Manzon Allah (S) ya koyar.
Akwai kuma yanayin da zai bada, ya zama an tsawwala wajen Sadaki, kamar yadda naga Iraniyawa kanyi wani lokaci, sabida yawan rabuwar Aure dake faruwa tsakanin wasu ba'adin nutane, sai a saka maka sadaki kamar Miliyan biyu ko uku, in za'a ɗaura aure ace ka kawo rabi. In kazo daga baya kace zaka saketa ayi-ayi ka dage matuqar matsalar ba ta ɓangaren ta bane, sai ace to, ai dama sadakin da ka biya rabi aka karba, cikaso rabin saika sake ta faqat.
Kaga in mutum ya tsaya yayi nazari ya kirfa, yanzu fa! In zan saketa suna nufin sai na cika kuɗin nan kenan, kuma daga baya inzo ince zan nemi wata, itama in sake bada wani sadakin. Kaga daga nan in yaga ba hanya saiya nemi a sassanta, to gashi nan dai wannan kuma wani lissafi ne, mai girman gaske. Don zan iya cewa adadin kuɗin yakai kimanin Sadakin aure Sayyada Zahra (SA). Allah ne Masani.. anan zan dakata
Allah ya tabbatar damu, ya bamu ikon yin biyayya gareshi, da gujewa hanyar saɓa masa komin ƙanƙancin ta.
Mu haɗu a rubutu na gaba......
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN