Hukumomi a Iran, sun ce alkalumman masu kamuwa da cutar covid-19 sun dan ragu cikin kwanaki shida a jere a kasar.
(ROHOTON ABNA24.com) Saidai da yake sanar da hakan yau Litini, kakakin ma’aikatar kiwon lafiya na kasar, Kianouche Jahanpour, ya yi gargadin cewa da sauren jan aiki a gaba kafin murkushe annobar.
Mutane 136 ne suka rasu sanadin cutar a cikin sa’o’I 24 da suka gabata a cewar hukumomin kiwon lafiya na kasar.
Mutane 2,274 ne aka sanar sun kamu da cutar a baya baya nan, wanda ya sanya adadin wadanda suka kamu a fadin kasar ya haura zuwa 60,500.
KARANTA:IRAN TA NUNA RASHIN AMINCEWAR TA GA AMURIKA NA CIGABA DA ZAMA A IRAQ
Ye zuwa ranar 31 ga watan Maris adadin wadanda suka kamu ya kai 3,111 sabanin yanzu da adadin ya ke yin kasa da hakan.
Kafin hakan dai shugaban kasar ta Iran, Hassan Rohani, ya yi kira ga ‘yan kasar dasu kiyaye tafiye tafiye wandanda ban a dole ba, a daidai lokacin da ya sanar da cewa za’a fara komawa bakin aiki daki-daki daga ranar 11 ga watan Afrilun nan.
KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya