@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADAN YA RAGE ALAMUN TASHIN ALQIYAMA SU CIKA
Tun Annabi (S.A.W.W)na raye yake cewa tashin alqiyams yayi kusa, kuma ya bayyanar mana da alamomin zuwanta.
An ruwaito daga Abu Ja'afar (A.S)yace;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Idan maza suka siffantu da mata, mata suka siffantu da maza,
Amincin mutane shine sallah (banda sallah ba su da wani abu da ke alamta muslimcinsu),
Suna bin sha'awace-sha'awace,
Suna sheqar da jinane,
Suna mu'amala da riba (kudin ruwa),
Suna bayyanar da zina,
Da gina dogwayen gidaje,
Suna halatta qarya,
Suna karbar rashawa (bribe),
Suna bin son zuciya,
Sunar sayar da addininsu da duniya,
Suna yanke zumunci,
KU KARANTA WANNAN 👇
☞ ͡Covid-19 Da Gwamnatin Nijeriya – Nazari
☞ ͡Wake son gafarar Ubangiji da dawwama cikin farin ciki??
☞ ͡Hijabi: Bin Umurnin Allah ya gagara ma wasu, bare na Donald Trump
Haquri ya kasance rauni (weak, ana yinsa ne bisa dole ba don Allah ba),
Zalunci kuma ya zama abin alfahari,
Shugabanni su zama fajirai,
Na kusa da su (waziransu)kuma maqaryata,
Wadanda aka amints da su kuma su zama maha'inta,
Da taimakon zalunci,
Makaranta (Qurra'u)su zama fasiqai,
Da bayyanar da zalunci,
Da yawaita sakin aure,
Da karbar shaidar zur,
Mata su wadatu da 'yan'uwansu mata,
A riqa mayar da dukiyar al'umma ta zama ganima (booty)
,
Bayar da sadaqa/imfaqi ya zama kamar haraji (tax)(a dole ake bayarwa),
Da nisantar mutanen banza saboda tsoron sharrin harsunansu (ba don Allah),
Da fitowar Safyani daga Sham,
Da Yamani daga Yemen (Safiyani da Yamani mutane ne masu da'awar Annabci),
Da shafe (halakar da wasu) mutane a wani guri da ake kira Baida'a,
Da yaqar Imam Mahdi (A.F)idan ya bayyana.‘’
Yanzu abinda ya rage shine bayyanar Annabawan qaryan nan da halakar da wadannan mutane da kuma bayyanar Mahdi (A.F).
A.I.G
~12th April, 2020.
KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa