Rbtw: Bin Haroun Sigau
Lallai, wannan karin magana batai ba, mu samman ta sabawa dan adamtaka, da Addinin Musulunci. Manzon Allah (S) ya gina mu akan son junan mu, da jajinta wa juna duk lokacin da wani abu ya sami ɗan uwan mu, alkairi ne ko sharri.
Yake cewa; "Imanin dayan ku baya cika, har sai ya soma ɗan uwan sa abinda yake soma kan sa."
Amma yanzun zamani, kio ince son ran mu ya saka, mun bijirewa wannan koyar wa ta addinin Musulunci, hasali ma, muna amfani da bangaran cin addini, wajen rarraba kawukan mu, da ƴan kazanci. Lokacin da Wandan nan Azzaluman mahukuntan Najeriya suka farmaki ƴan uwan mu a Zaria (ZariaMassacre) wasu ba'a din Musulmi fito wa sukai suna cewa; masha Allah, wannan aiki na Gwamnati yana kyau, sun fara tage mana hanya" shin wannan wannan sunnar wanene kuka ɗauja nasa dai baya daga koyarwar Manzon Allah.
Amma cewa suke; su masu bin sunna ne, to, sunna dai iri-iri ce, akwai ta makiya Allah da kuma ta masoya Allah na Hakika, bamu san wacce suke bi ba, sun manta ita bala'i in ta afku, ko ta kama afkuwa, wajibin ka ne ka ɗau matakin ganin ka sauke nauyin dake kanka na wanda wannan bala'i ke faruwa dasu, ta hanyar hana ci gaban bala'in ne, ko kuma shawarwari da yi musu addu'a.
Sai yanzu gashi, waɗan da suke ikirarin sun rage musu aiki, son kawar da Shi'a sun dawo ta kan uban kowa, basu ware ɗaya ba, Sunna kake, Shi'a, ko Ba Salafe. Kowa gasa masa aya a hannu suke a wannan ƙasa, sun kulle mutane ba abinci da sunan kariya daga cuta, alhali basu taimaki kowa ba, sun bar talakawa da yunwa da kuncin rayuwa.
Wanda in Cutar da ake gudu bata kashe mutum ba, yunwa zata kashe shi, sabida ba abinci, babu kuma abin sayen abincin. Lokacin da Almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gaya wa al'umma, cewa; wannan gwamnati ba mafita bace, ba kuma zasu taɓa yi muku adalci ba, al'umma gani suke gabar Ƴan Shi'a dasu ne yasa suke faɗar haka, alhali, su suna tunasar da mutane ne don sauke nauyi gudun kada mutane suyi ta bin azzalaumai a makance. Domin duk wanda ya goya wa azzalumi baya wajen zalunci, ranar lahira za suyi tarayya da juna bisa alhakin wannan zalunci ɗin.
LATSA NAN👇
☞ ͡Ku cika azumin ku, zuwa dare" – Faɗar Allah (T)
☞ ͡Iyali A Muslunci... Fita Na Uku (3)
☞ ͡Hukuncin Shan Ruwa
Takai ada cen in kana la'antar azzaluman nan, har wanda ma bai taba zuwa Islamiyya, ko makarnta ba, saika ji ya fara ma wa'azi akan abinda bai sani ba, yana cewa "Babu kyau zagin Shugabanni". Domin shi haka yake ji a wajen Malaman fada. To, mu dama tun farko abinda muke gudu muku kenen, ihu bayan hari, gashi yanzu zagin azzalaumai ya zama wuridin ƴan Najeriya, sabida kowa yana ji a jikin sa.
Wanda da tun cen baya mun gane su, mun kiyaye yi musu biyayya, munce mu addini kawai muke so yayi iko damu a shari'an ce kmaat yadda Manzon Allah yazo mana dashi, kuma mu ginu da aikata ayyuka na Kwarai, da yanzun tafiyar mu tayi nisa. Wannan shine kiran da Sayyid Zakzaky (H) yake tayi tsawon shekaru arba'in (40) ba dare ba rana, burin sa ya wanke kwakwalen mu, ya cire maguzanci da ƙabilancin dake damun mu, mu zama fes, mun ɗamfaru mun zama Musulmi na haƙiƙa.
Har yanzun bamu makara ba, kofa a bude take, Musulmi da Kiristocin mu, mu haɗu mu zam abu guda wajen kauda zalunci da kuma tabbatar da adalci. Zakzaky kiran sa bai ware kowa ba, kamar yadda addini ba wani hukunci da baizo mana dashi ba, ta hanyar yadda zamu zauna dako wani irin mutum, musulmi yake ko kirista. Addinin Musulunci shine addinin daya zo da adancin da babu wani wanda zai zauna kusa da ma'abocin sa baiyi sha'awar sa ba, domin addini ne da aka gina tubalin sa da gaskiya.
Saidai mune muka gurɓata shi, da munanan ayyukan mu. Ya zamu yi mu dawo da addinin nan?? Amsa: Ta hanyar Gyara kai, kyawawan ɗabi'u, domin in abin ace yanzu daula ta kafu a wannan nahiya, ya zama kuma bamu gyara ayyakan mu ba, to, zai zama mun fitinu, domin Addini zai zama yana ƙalubalan tar mu ne, kuma yana hukunta mu bisa munanan ayyukan mu. Hakan ma baya yiwuwa (Addini ya kafu) ba tare da al'umma ta gyaru ba.
Shiyasa, kullum Malam (H) in yana magana damu zaga ji yana cewa; "kamar lokaci yayi, amma mune bamu shirya ba'" kunga kenen yanzu aikin daya hau kan mu shine kyautata alaƙar mu da Allah, in muka gyara tsakanin mu da Allah, sai Allah ya gyara tsakanin mu da mutane, ya saita mana komi ya zama lebir..
Fatan Allah ya saka mu amfana da wannan ɗan rubutu, ya kuma kwato mana Jagoran mu, Jagoran Gaskiya Sheikh Zakzaky (H) a hanun Azzalumai, ya bashi lafiya da nisan kwana, mu kuma ya saka mu cikin mataimaka Imam (Atfs) a haƙika.
#AllahProtectZakzaky
#JusticeForZakzaky
#FreeZakzaky
#JusticeOnly
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Jagoran Gaskiya