@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
NASABARSA DA HAIHUWARSA (A.F)
Shine Muhammad Al-Mahdi, Ibn Alhassan Khalis (Askari)Bn Aliyu Al-Hadi Bn Muhammad Jawwad Bn Aliyu Al-Ridha Bn Musa Al-Kazeem Bn Ja'afar As-Sadiq Bn Muhammad Baqir Bn Aliyu Zainul-Abideen Bn Hussaini Bn Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S).
MAHAIFIYARSA :- Ita ce Narjis, ana ce mata Susan ko Hudais, amma mafi shaharar sunan nata shine Narjis (S.A). Baqar fata ce kuma mutunitar Afrika.
An haifi Imam Mahdi (A.F)ne ranar 15 ga Sha'aban, shekara ta 256 bayan Hijrah (B.H).
ALKUNYARSA:- Ita ce Abu Qaseem.
LAQABINSA:- Laqabunsa (A.F)na da yawa, amma dai ga su kamar haka;
-IMAMU BIL-HUJJAH (Shugaba hujjar Allah a doron qasa)
-KHALAFUS-SALIHU (Salihi mai maye gurbin Annabta)
-AL-QAA'EEM (mai tsayar da adalci bayan cikar duniya da zalunci)
-ALMUNTAZAR (wanda ake sauraron bayyanarsa)
-SAHIBUZ-ZAMAAN (ma'abocin zamani jagora kan kowa).
Mafi shahara daga cikin laqabun nasa shine AL-MAHDI (A.F).
Wannan haihuwar tasa ta kasance ne a zamanin daular Abasiyawa, wanda ya taso tare da MU'UTAMID babban da ga MUTAWAKKIL (Mu'utamid is the eldest son of Mutawakkil).
Bisa gallazawa daga Abasiyawa da kuma ganin dama ta Allah yasa Imam (A.F)ya shiga Ghaiba (went for refuge)a wani guri da ake kira (SURRA-MAN-RA'AH)a shekara ta 265, lokacin yana da shekaru 9 kenan a duniya.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~5th April, 2020.
-