Imam Mahadi (Ajtfs) (5)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

FALALAR ALLAH MAI WANZUWA CE MAFI ALKHAIRI GARE KU

Yayin da Imam ya bayyana, zai jingina bayansa (his back)a jikin Ka'abah, kuma sannan mutane 313 daga mabiyansa su taru gare shi.

To, za a sami tawagar jama'a daban-dabam da za suyi nufin yaqarsa, sai dai ba za suyi nasara ba.

Ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W.W)yana cewa;

LATSA NAN👇
Ranar lafiya ta duniya: Qalubale ga gwamnatin Nijeriya
Happy birthday to the golden son of 21st century Sheik Zakzaky
Imam Mahadi (Ajtfs): Wacce tambaya kake tsoro Imam yayi maka???

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ WATA JAMA'A ZA TA YAQI KA'ABAH, AMMA IDAN SUKA ISO WANI GURI DA AKE KIRA BAIDA'A TSAKANIN MAKKAH DA MADINAH ZA A KISFE NA FARKONSU DANA QARSHEN SU....‘’

Lalle wannan abu bai faru ba a tarihi, sai bayyanan Imam (A.F)hakan za ta faru, yayin da suka fito da nufin yaqarsa sai Allah ya shafe su.

Sannan kuma wata tawagar da za ta yaqe shi za ta riske shi a ne a tsakanin RUKUNUL-YAMAN da MAQAAMA IBRAHEEM.

Farkon abinda zai fara fitowa daga bakinsa (A.F)ita ce wannan ayar;

‘’ BAQIYYATULLAHI KHAIRUL-LAKUM IN KUNTUM MU'UMINEEN (Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alkhairi gare ku idan kun kasance muminai...)!‘’

(Suratul-Hud, aya ta 86)

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN Daga nan kuma sai yace;

‘’ NINE FALALAR ALLAH MAI WANZUWA, KHALIFANSA KUMA HUJJARSA A KANKU !‘’

 Babu wanda zai sallama gare shi face yace;

‘’ AMINCI YA TABBATA A GARE KA YAA FALALAR ALLAH A DORON QASA !‘’

A yayin da adadin wadanda suka taru a gurinsa suka kai misalin dubu goma (10,000), to, babu wanda zai rage daga Bayahude ko Banasare ko kuma wani mai bautar wanin Allah face yayi imani kuma ya gaskata.

Sai tafarki ya kasance tafarki daya (1)na muslimci. Kuma duk wani abu da ya kasance shi ake bautawa a doron qasa koma bayan Allah, wuta za ta sauka a kansa daga sama ta qone shi .

Don ganin wannan bayani a duba

(NURUL-ABSAAR FEE MANAAQIBI AHLUL-BAITIN NABIYYI, NA ASSHEIK MU'UMINU BN HASSAN MU'UMINU ASSHIBALANJI, SHAFI NA 278)

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~9th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post