@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WASU FA'IDODI GAME DA SHI (A.F)
Akwai fa'idodi da suka shafe shi (A.F)wadanda ya kamata a sani kuma a nazarce su sosai cikin al'amarinsa.
Ga sunan kamar haka yadda suka zo cikin wani littafi me suna (SAWAA'IQ);
(1)- Abinda ya bayyana kuma yafi shahara shine, lalle fitowar Mahdi (A.F)daga ghaiba za ta kasance ne kafin dawowar Isah Almasihu (A.S)kamar yadda ya tabbata daga Ma'aiki (S.A.W.W),
‘’ YA ZA KU KASANCE YAYIN DA 'DAN MARYAMA YA SAUKO ALHALI LIMAMINKU NA TARE DA KU ?‘’
(2)-Lalle shi yana daga cikin Ahlul Bait (A.S)ne ba daga wani gidan ba. Kamar yadda yazo daga Annabi (S.A.W.W);
‘’ QIYAMA BA ZA TSAYA BA HAR SAI WANI MUTUM DAGA IYALAN GIDANA YA YI MULKI.....‘’
(3)- Lalle shi zai taimakawa Isah (A.S)wajen kashe Dujal a qofar Laddu a qasar Palestine dake Sham.
(4)- Kuma zai fito ne cikin shekarar wutri.
Misali:- 1, 3, 5, 7, 9. Ba 2 ko 4 ko 6 da misalinsu ba.
KARANTA NAN👇
◉Sister a social Media Fita na Daya (1)
◉Nazari akan Rayuwar Aure Fita Na Biyu (2)
◉Dokoki 17 da ke kan mace saliha Na (16)
◉Hikima kayan mumini Fita Na Huɗu (4)
(5)- Za ayi masa mubaya'a ne a garin Makka, zai tafi daga gare ta zuwa Kufah (garin da Imam Ali ya zauna ya shimfida daular adalci), sannan ya rarraba rundunarsa ta adadin jama'ah 313 gwargwadon adadin mahalarta yaqin Badr.
(6)- Adadin shekarunsa da zai yi bayan tasowarsa ita ce shekara 10, wato zai rayu tsahon shekara 10 bayan bayyanarsa. Kamar dai yadda Annabi (S.A.W.W)ya bayyana cikin wani hadisi.
‘’........HALITTUN SAMMAI DA QASSAI DA MA TSUNTSAYE ZA SU YARDA DA KHALIFANCINSA, KUMA ZAI YI MULKI (tsahon)SHEKARA 10 .‘’
(7)- Kuma lalle ikonsa (mulkinsa) zai kai mahudar rana da mafadarta. Za a bude masa taskoki , babu wani abu rushasshe da zai rage a doron qasa face ya rayar da shi (kafin ayi tashin qiyama wanda zai rushe komai da kowa).
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Daga wakilanmu na Bauchi zone.Tare da Ado Isah Guda.
09039791509-08126385470
~7th April, 2020.