Imam Mahadi (Ajtfs) (3)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BAYYANARSA ALAMA CE TA TASHIN ALQIYAMA

Bayyanarsa na daga cikin manyan alamu na tashin alqiyama wanda Allah (T)ya ambata.

Muqaatil Bn Sulaiman da ma wadanda suka biyo shi cikin masu Tafsirin fadin Allah (T);

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ LALLE SHI(dawowar Mahdi)ALAMA CE TA TASHIN ALQIYA .‘’

(Suratul-Zukruf, aya ta 61)

Muqaatil yace; ‘’ Ai Mahdi ne, zai kasance a qarshen zamani .‘’

Akwai wata tawaga mai duhu da za ta fuskanto daga Kurasan dauke da baqar Tuta wacce Imam Mahdi ke cikinta. Wannan baqar Tutar ta kasamce wata alami da ke bayyana bayin Allah.

KARANTA NAN👇
Sister a social Media Fita na Daya (1)
Nazari akan Rayuwar Aure Fita Na Biyu (2)
Dokoki 17 da ke kan mace saliha Na (16)
Hikima kayan mumini Fita Na Huɗu (4)

Hafiz Abu Na'eem ya fitar daga Thauban (R.A)yace, Manzon Allah (S.A.W.W)yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ IDAN KU KA GA BAQAR TUTA TA FITO DAGA KURASAN, TO, KU JE MATA KO DA DA JAN CIKI NE (rub-da-ciki)AKAN QANQARA (ice), DOMIN A CIKINTA AKWAI KHALIFAN ALLAH ALMAHDI .‘’

Sannan kuma shi wannan Khalifa na Allah (Almahdi)shine babban jagora wanda zai kawar da zalunci.

Kamar yadda ya tabbata cikin Bukhari da Muslim , daga Abdullahi Bn Abbas (R.A)yace, na ji Manzon Allah (S.A.W.W)na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ WATA JAMA'A DAGA AL'UMMATA BA ZA GUSHE BA TANA YIN YAQI (gwagwarmaya)AKAN GASKIYA, SUNA TSAYE QYAM (babu canzawa)HAR RANAR ALQIYAMA. ISAH 'DAN MARYAMA DAGA CIKIN ANNABAWANMU ZAI SAUKO, SAI SHUGABANSU (Mahdi)YACE; ‘’ KAYI MANA SALLAH .‘’

SAI YACE; ‘’ A'A, INAH ! AI SASHENKU AKAN SASHE SHUGABANNI NE WADANDA ALLAH YA KARRAMA WANNAN AL'UMMA DA KU .‘’

Dangane da cewa Imam Mahdi (A.F)shine jagora akan kowa har ma da Isah (A.S), Abu Huraira ya kawo wani hadisi yace, Manzon Allah (S.A.W.W)yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ YA ZA KU KASANCE YAYIN DA 'DAN MARYAMA YA SAUKO CIKINKU, KUMA LIMAMINKU NA TARE DA KU ?‘’

Duk wadannan hadisai ne da ke nuna mana cewa Imam Mahdi (A.F)zai dawo, kuma za suyi aikin kawar da zalunci ne tare da Annabi (A.S), sannan kuma ni'ima ta biyo baya bayan an kawar da zalunci tare da tsayar da adalci.

Kamar yadda 'Dabarani ya fitar cikin MU'UJAM nasa, daga Abu Sa'idul Khudriy (R.A), daga Annabi (S.A.W.W)yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ AL'UMMATA ZA TA NI'IMTU A ZAMANIN MAHDI DA NI'IMAR DA BA A TABA YIN IRINTA BA (a tarihin duniya). SAMA ZA TAYI RUWAN (albarka)A KANSU, KUMA QASA BA ZA TA RAGE WANI ABU DAGA TSIRONTA BA FACE TA FITAR DA SHI .‘’

(Nurul-Absar, sh;277)

MARABA DA WANNAN JAGORA MAI NI'IMTAR DA DUNIYA !

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

             09039791509

~8th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post