Ilmun Nafs (psychology) a cikin Qurani






 علم النفس القرآن الكريم

(KASHI NA 1)

Abbagano✍

Allah (t) ya bamu labari a cikin Alkur'ani mai girman ɗauka ka,akan siffar aljannar da akai wa المتقين (masu taƙawa).


( وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )

آل عمران (133) Aal-Imran

Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.

SEDE MENE SUFFAR WADAN NAN MASU TAƘAWAR?

Allah yabamu labarin su a yar datake bin ayar sama.


( الَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ )

آل عمران (134) Aal-Imran

Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.


WANNAN AYAR TA HAƊA ABUBUWA GUDA UKU NA AYYUKA.

1- na farko:- shine bayar da sadaka na dukiya ga mabuƙata, wanda malami suka lissafa hakan cikin abubuwan da suke saka Rai (النفس) tasamu tabbatuwa.

الَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ

2- na biyu:- yanda mutum zai koyi kashe wutar da take harzuƙashi, (fushi) ta duk wata hanya dazata zigashi ɗaukar mataki akan wasu.

وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ

3- na uku:- wannan ayar ta nuna mana yadda zan a koyi yiwa juna uzuri, malamai na ilmun nafsi suna cewa:- yiwa juna uzuri shine babbar hanyar kashe wutar zuciya.

وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ )


MUTAHO ZUWA AYAR GABA!!!


( وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَن يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَىٰ مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ )

آل عمران (135) Aal-Imran

Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane.

ITAMA WANNAN AYAR TA TATTARO ABUBUWA GUDA UKU

1- yarda da lefi (kayar da kayi lefi) lokacin da mumini ya aikata alfasha,ko ya zalunci kansa, yazama wajibi yayi gaggawa yagano kuskuren sa, ya kuma kiyaye shi.

ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ

Neman gafara gurin Allah (t) yana nuna wa bawa yayi lefi kuma ya yarda da lefin sa.

2- yaƙini akan wannan lefin zai yiwu a gyara shi,malaman ilimin nafs sun tabbatar cewar yaƙinin mara lafiya akan zai saku waraka,yana daga cikin rabin silar warkewar sa.

وَمَن يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ
Imanin mumini akan Allah (t) shine kaɗai mai gafar ta zunubai.

3- malaman ilimin nafs sunce:- mutum yasamu cikakken iko na rashin sake aikata wani laifin

وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَىٰ مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ

mu haɗu kashi na biyu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post