@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
QALUBALE GA AL'UMMAR MUSULMI
Gaskiya na ji kunya (shame)da takaici (disgrace)yayin da yayi min wata tambaya game da raunana (tsofin)cikimu.
Akwai wani inyamuri (Ibo)wanda nake yawan zuwa shagonsa don sayen magani, duk da cewa bai san sunana ba amma dai ko ina ya ganni ya sanni sakamakon zuwa shagonsu da nake yi.
Wata rana na je shagonsa don sayen magani sai ga wata tsohuwar mata tazo tana yin bara, sai yace tayi haquri, ni kuma na bata murtala (#20).
Bayan tafiyarta sai yace min,
‘’ TUN DA DAI MUN DADE TARE MUN ZAMA 'DAYA, WATA TAMBAYA NAKE SON YI MAKA GAME DA MUTANENKU .‘’
Nace masa, me ya faru? Sai yace;
‘’ NI INA YAWAN GANIN IRIN WADANNAN MUTANE NAKU NE SUNA BARA, WASU MA SAI KA JI ANA KIRANSU ALHAJI. MU KUMA MUNA 'DAUKA DUK WANDA KA JI ANA KIRANSA ALHAJI TO, MAI KUDI NE.‘’
Nace masa, gaskiya wannan tambayar tasa tana da ma'ana (amfani).
Sai na ba shi amsa da cewa, to, gaskiya dai babban dalilin da yasa yake ganin mutanen mu na yawaita yin bara da tsufarsu bai wuce abubuwa biyu ba.
(1)- Wasu za ka tarar sun tsufa ne kuma suna da yara qanana wadanda ba za su iya daukar nawinsu ba, saboda haka a dole suke fita don neman abinda za su ci da iyali nasu da sauran buqatun yau-da-kullum.
(2)- Wasu kuma tsananin son abin duniya ne suke son tarawa da rashin godiya, amma ba su rasa 'ya'ya masu daukar nawinsu ba.
Sai kuma wani dalili na uku (3)a matsayin qari, shine rashi taimakon daga maau kudin mu.
Domin da ace masu kudin cikinmu suna duba raunana suna taimaka musu taimako na gaskiya ba suna ba, to, da ba za sami yawan irin wadannan mabarata ba.
Yace, ‘’ KAI, MAGANARKA GASKIYA NE!IN HAKANE KUWA, TO, MUTANENMU SUN FI NAKU GODIYA DA KYAUTATAWA, DOMIN MUMA MUNA DA IRINSU AMMA BA MA BARINSU SUNA YAWON BARA, KUMA SUNA HANUWA .‘’ -
Gaskiya na ji kunya sosai har ma na rasa abinda zan qara gaya masa, domin ni a dabi'ata ba na son lullube gaskiya don wanke mai laifi.
Wannan babban qalubale ne gare mu musulmi!
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509-08126385470
~4th April, 2020.
Tags:
Daga marubata