_*Abbagano✍*_
_👉Sai ka lura duk mutumin da kudine yasa kasiyeshe,to kasa aranka waninka ma zai iya Siya sa._
_👉Yadda muke da maqabartar bunne matattu,yazama wajibi mutanadi maqabartar binne laifukan masoyanmu._
_👉“Idan kasan yadda mutane ke saurin manta wanda ya mutu, ba zaka damu da cewa dole sai ka burge wani ba.”_
_👉Yayinda kaga mutane suna gudunka ahalin tsanani,to ka gane Allah ne ya jibinci lamarinka sai ka koma gareshi._
_👉Yin shiru a wasu guraren bawai rauni bane._
_Kai!!shine ma dede saboda kar murasa kimar kanmu a gaban masu munanan hali_
_👉Dan uwa kamar misalin ido ne da hannu.idan abu yashiga idon ka hannu ke temaka maka. idan hannu yayi rauni ido ke taya shi kuka_
_👉Baa gane haqiqanin mutane har sai an jarrabasu,bakaga yadda gishiri yayi kama da sukari ba!Se a baki ake ganesu_
_👉Wadan da suka jefa yusufu a rijiya,su suka durqusa gabansa suna roqonsa da yayi musu Sadaqa ,kar wulaqancin mutane ya dameka._
_👉Gishirin teku baya canzawa komin yawan ruwan sama. ka zamo kamar teku maganganun mutane baza suyi tasiri akanka ba_
Tags:
Muhimman zantuka